An cafke wani Mutum da laifin lakadawa Agolansa duka har Lahira a jihar Edo

An cafke wani Mutum da laifin lakadawa Agolansa duka har Lahira a jihar Edo

A yayin da Hausawa kan ce tsautsayi ba ya wuce ranarsa ya auku kan wani Mutum, Mathias Otabor da tuni ya shiga hannun hukumar 'yan sanda bisa aikata laifi na lakadawa Agolansa duka har lahira can jihar Edo dake Kudancin Najeriya.

Ajali ya fada kan wannan Agola mai shekaru uku kacal a Duniya, Destiny Meshack, kamar yadda shafin jaridar The Nation ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari ya auku ne a gida mai lamba 8 dake kan hanyar Obanosa a babban birnin jihar Edo watau Benin.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Babatunde Kokumo, ya bayar da tabbacin aukuwar wannan lamari da cewa, Mista Otabo ya lakadawa Agolansa duka ne har sai da ya yi shame-shame kasa wanwar kana ya ce ga garin ku nan.

An cafke wani Mutum da laifin lakadawa Agolansa duka har Lahira a jihar Edo

An cafke wani Mutum da laifin lakadawa Agolansa duka har Lahira a jihar Edo
Source: Facebook

Tuni dai an killace gawar Marigayi Destiny a dakin ajiyar gawa dake babban Asibitin jihar Edo a yayin da hukumar 'yan sandan ke ci gaba da gudanar da binciken ta.

Kokumo ya bayyana hakan ne a yayin gabatarwa manema labarai wasu miyagun 'yan ta'adda 76 da suka aikata laifuka daban-daban kama daga kisan kai, garkuwa da mutane gami da fyade 'ya'ya Mata.

KARANTA KUMA: An garkame wata Uwargida da laifin bincike cikin Wayar Salula ta Mai gidan ta

Cikin wadannan miyagun mutane da hukumar 'yan sandan ta cikwikwiye sun hadar da wani Mutum mai sunan Moses da ya shiga hannu bisa laifin yiwa diyarsa 'yar shekara 13 fyade.

A yayin bayyana takaicinta dangane da wannan cin zarafi da keta ma ta haddi, ta bayyana cewa mahaifin na ta ya yi barazanar batar da ita daga doron kasa muddin ta bayyanawa wani mahaluki wannan aika-aikar da ya yi ma ta.

Kwamshinan 'yan sandan ya kara da cewa, nan ba da jimawa ba za a gurfana da wannan miyagun mutane gaban Kuliya da zarar sun kammala binciken su.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel