Satar Naira biliyan 1: Wani tsohon gwamna a Arewa ya bakunci kotu don shari'a

Satar Naira biliyan 1: Wani tsohon gwamna a Arewa ya bakunci kotu don shari'a

- Wani tsohon gwamna a Arewa ya bakunci kotu don shari'a

- Sunan tsohon gwamnan Saidu Dakingari

- Kotun ta bayar da belin sa kan Naira miliyan 10

Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Saidu Dakingari a ranar Laraba ya gurfana a gaban Alkalin babbar kotu ta biyu dake zaman ta a garin Birnin Kebbi, jihar Kebbi sakamakon karar da hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kasa watau Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission, (ICPC) a turance ta shigar.

Satar Naira biliyan 1: Wani tsohon gwamna a Arewa ya bakunci kotu don shari'a

Satar Naira biliyan 1: Wani tsohon gwamna a Arewa ya bakunci kotu don shari'a
Source: Twitter

KU KARANTA: Dan majalisa a Arewa ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa

Kamar yadda muka samu, hukumar ta Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission, ICPC dai ta gurfanar da tsohon gwamnan ne a gaban kotun tana tuhumar sa da yin sama da fadi da dukiyar jihar da ta kai Naira biliyan N1,094,320,000 lokacin da yake gwamna.

Legit.ng dai ta samu cewa Alhaji Sa'idu ya musanta zarge-zargen da aka yi masa inda ya bayyana cewa shi bai da hannu a hakan.

Alkalin kotun dai ya bayar da shi beli akan kudi Naira miliyan 10 zuwa ranar da za'a cigaba da shari'ar.

A wani labarin kuma, mun samu cewa tsohon gwamnan jihar ta Kebbi ya sayi fom din takarar kujerar dan majalisar wakilai a jam'iyyar APC a zaben nan na 2019 mai zuwa.

Wannan dai ya zo wa jama'a da dama a ba zata musamman ma ganin cewa shine ya zama gwamna na farko da ya fara yin hakan inda a baya gwamnoni kan zabi tafiya majalisar dattawa ne bayan kammala wa'adin mulkin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel