Tsufana ba zai iya barina jure rashin d'ana ba - Mahaifiyar Manjo Janar Alkali

Tsufana ba zai iya barina jure rashin d'ana ba - Mahaifiyar Manjo Janar Alkali

- Akalla makwanni hudu kenan, al'ummar Unguwar Bolawa ke cikin jimamin bacewar Manjo-Janar Mohammadu Alkali (mai ritaya)

- Mahaifiyarsa Hajiya Halima Alkali Umaru, ta ce tana matukar son jin muryar yaronta da sanin halin da yake ciki

- Ta ce a yanzu da ta ke dosar shekaru 94, ba zata iya jure rashinsa ba

Akalla makwanni hudu kenan, al'ummar Unguwar Bolawa, Fatisukum, kusan kilomita 104 daga Damaturu, jihar Yobe, ke rayuwa cikin jimami da tu'ajjabin bacewar Manjo-Janar Mohammadu Alkali (mai ritaya). Har zuwa yanzu, jama'ar garin na zama a gungu-gungu, don tattaunawa kan wannan lamari mai tsantsar rikitarwa.

Kamfanin jarida na DailyTrust, ya samu damar zuwa gidan sanannen mutumin nan Alkali, mahaifin Janar Idris, inda ya gana da mahaifiyarsa mai shekaru 93, Hajiya Halima Alkali Umaru, mahaifiyar Manjo Janar, wanda shine tsohon shugaban sashen gudanarwa na rundunar soji, wanda kuma shine yaronta na 8.

Ta yi maganganu masu tsuma zuciya, tare da rokon gwamnati data dawo mata da yaronta ta kowane hali, kasancewar a wannan tsufan nata na shekaru 93, ba zata iya jure rashinsa ba.

KARANTA WANNAN: PDP ta nisantar da kanta daga zaben fidda gwani na jihar Kano da Kwankwaso ya jagoranta

Manjo-Janar Idris Alkali da ya bace tare da motarsa da aka gano a kududdufin Du

Manjo-Janar Idris Alkali da ya bace tare da motarsa da aka gano a kududdufin Du
Source: Twitter

Hajiya Halima ta ce yunkurin da rundunar soji suke yi na gano yaron nata abun a yaba ne, sai dai ita babban burinta shine ta san halin da ya ke ciki, walau a raye ko a mace, idan yana da rai ya dawo gareta, idan kuwa baya raye, to ko gawarsa ce ta gani ko hankalinta zai dawo jikinta.

"Ina matukar son jin muryarsa," ta bayyana hakan cikin yanayin kuka.

Ko da aka tambayeta ko akwai wanda ya taba tuntubarta tun bayan bacewarsa, sai cewa tayi: "Sau tari nakan dinga gayawa kaina cewar baya hannun masu garkuwa da mutane saboda tun bayan bacewarsa, babu wanda ya bukaci neman kudin fansarsa.

Tsufana ba zai iya barina jure rashin d'ana ba - Mahaifiyar Manjo Janar Alkali

Tsufana ba zai iya barina jure rashin d'ana ba - Mahaifiyar Manjo Janar Alkali
Source: Twitter

KARANTA WANNAN: Sabuwar nasara: Rundunar sojin sama ta tarwatsa mabuyar mayan Boko Haram a Borno

"Bari na sanar da ku gaskiya, tunda aka haife ni, ban taba tsintar kaina a cikin wani mawuyacin hali kamar na bacewar yarona ba. Yanzu dai shekaruna 93, ina dosar 94 amma wannan lokacin ne mafi muni ga rayuwata."

Ta ce wadanda suka aikata hakan ga yaron nata, wata-kila ko basu san adadin shekarunta ba da kuma halin data tsinci kanta a ciki, tana mai rokonsu da su dawo mata da yaronta kasancewar "na tsufa yanzu, ba zan iya jure rashin sa ba, ba zan iya jure wannan balahirar ba."

"Rana ta karshe da nayi magana da shi itace ranar da ya bace. Na yi kokarin kiransa a waya don jin muryarsa amma wayar bata shiga. Na kira matarsa don ta sadani da shi, amma tace a lokacin yana kan hanyar zuwa Bauchi. Na yi alkawarin kiransa da zaran ya isa."

Mahaifiyar babban jami'in sojin, ta kuma roki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da rundunar soji ta kasa, da su taimaka su dawo mata da yaronta, kasancewar ya shafe sama da shekaru 35 yana yiwa kasarsa hidima.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel