Da duminsa: Rikici ya barke a wurin zaben fitar da 'yan takarar majalisar wakilai a PDP a jihar Delta

Da duminsa: Rikici ya barke a wurin zaben fitar da 'yan takarar majalisar wakilai a PDP a jihar Delta

Rahotannin da muka samu daga shafin Channels tv ya tabbatar da barkewar rikici a wajen zaben fidda gwani na 'yan majalisar wakilai na tarayya na jam'iyyar PDP a jihar Delta.

Majiyar ta ce an ta harbe-harben bindiga wanda hakan yasa wakilan jam'iyyar masa kada kuri'a duk suka gudu daga harabar inda ake gudanar da zaben.

Da duminsa: Rikici ya barke a wurin zaben fitar da 'yan takarar majalisar wakilai a PDP a jihar Delta

Da duminsa: Rikici ya barke a wurin zaben fitar da 'yan takarar majalisar wakilai a PDP a jihar Delta
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dan Sule Lamido ya lashe takarar kujerar Sanata a PDP

An fara rikicin ne yayin da wasu wakilan jam'iyyar suka fara tafka muhawara mai zafi a wajen zaben.

Daga baya kuma lamarin ya janyo fada tsakaninsu hakan yasa jami'an tsaro suka garzayo wajen da ake zaben suna harba bindiga a sama domin kokarin kawo karshen rikicin.

A halin yanzu dai ba'a san takamamen abinda wakilan jam'iyyar ke musu a kai ba.

Ku biyo mu domin karin bayani...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel