Mu ke kare Saudiyya, idan muka cire taimakonmu na makonni biyu za’a tsige ka – Trump ya caccaki Sarki Salman

Mu ke kare Saudiyya, idan muka cire taimakonmu na makonni biyu za’a tsige ka – Trump ya caccaki Sarki Salman

Shugban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce kasar Saudiyya da shugabanta ba zasu yi makonni biyu da rai ba idan kasar Amurka ta janye taimakon da take bata.

Donald Trump ya bayyana wannan abu ne a wani taro a garin Mississippi a kasar Amurka.

Yace: “Mu ke kare Saudiyya. Za suyi alfaharin sunada arziki ne? Amma ina son Sarki Salman. Amma fa ina mai cewa – Mu ke kareku – indan muka janye taimakonmu ba zaka kasance kan mulkinka ba cikin makonni biyu,”

Trump ya yi wannan jawabi ne bisa ga tashin farashin kudin danyen mai da ke kara tashin gwauron zabo a Amurka.

KU KARANTA: Akan Shehu Sani? El-Rufa’I yana ganawar gaggawa da shugaba Buhari

Kasar Saudiyya ce kasa mafi arzikin man fetur kuma shugabar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC.

Trump ya yi kira ga sarki Salman a ranan Asabar domin tattauna yadda zasu tsagaita kasuwan man fetur domin cigaban tattalin arzikin duniya, game da cear kafar sada labarai ta SPA.

Yarima mai jiran gado, Mohammad bin Salman ya tafi kasar Kuwait a karshen makon da ya gabata domin tattaunawa da sarkin Kuwait, Sabah Ahmed Al Jabir, kan kara fitar da man fetur.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel