Akan Shehu Sani? El-Rufa’I yana ganawar gaggawa da shugaba Buhari

Akan Shehu Sani? El-Rufa’I yana ganawar gaggawa da shugaba Buhari

Labarin da ke shigowa da duminsa na nuna cewa gwamnan jihar Kaduna, Naisr Ahmed El-Rufa’I da gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, sun shiga ganawar sirri da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ta Aso Rock, Abuja.

Gwamnonin biyu sun isa fadar shugaban kasan ne misalin karfe 3:15 na ranan nan.

Har yanzu suna cikin ganawar yayinda muke kawo muku wannan rahoto.

Za ku tuna cewa gwamnan jihar Kadunan na cigaba da hamayya da Sanata Shehu Sani tun kimanin shekaru uku yanzu. A yayinda zabe ya gabato, sanatan ya nemi ayi sulhu amma gwamnan yace ba zai yard aba sai ya sauyashi.

KU KARANTA: Kwamitin zantarwan jam'iyyar APC ta yi watsi da zaben fidda gwanin jihar Legas

Hakan ya sanya Sanatan ya nemi agajin jam’iyyar APC ta kasa domin sulhuntasu. Mataki na farko na yin sulhu shine cire takunkunmin da jam’iyyar ta sanya masa a matsayin dan jam’iyya, amma bangaren jam’iyyar ta jiha ta nuna rashin amincewarsa da wannan afuwa.

Daga karshe yayinda ake shirin gudanar da zaben fidda gwanin kujerar sanata maso tsakiya na jihar, jam’iyyar ta kasa ta baiwa Sanata Shehu Sani goyon bayan yayi takara shi kadai yayinda taki tantance wanda gwamna El Rufa’I, wanna abu ya jawo tashin hankali da zanga-zanga a jihar

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel