Da duminsa: Gwamnan APC ya fadi zaben cikin gida, ya taya wanda ya kayar da shi murna

Da duminsa: Gwamnan APC ya fadi zaben cikin gida, ya taya wanda ya kayar da shi murna

Akinwunmi Ambode, gwmnan jihar Legas ya gaza kai bantensa a zaben fitar da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC.

Babajide Sanwo-Olu, abokin hamayyar Ambode, ne ya yi nasarar lashe zaben na fitar da dan takarar gwamnan, kuma yanzu ta tabbata shine dan takarar gwamnan jihar Legas a karkashin jam'iyyar APC.

Bayan sanar da sakamakon zaben, gwamna Ambode ya taya abokin hamayyar tasa, Sanwo-Olu, murnar nasarar da ya samu, a wani takaitaccen jawabi da ya yi a yau, Laraba, bayan sanar da sakamakon zaben.

A jawabin nasa, Ambode ya bayyana cewar zai goyi bayan Sanwo-Olu domin tabbatar da samun nasarar jam'iyyar APC a zabukan 2019.

Da duminsa: Gwamnan APC ya fadi zaben cikin gida, ya taya wanda ya kayar da shi murna

Ambode
Source: Depositphotos

Jawabin na Ambode ya matukar bawa jama'a mamaki, domin an yi tunanin zai nuna fushinsa ne bisa faduwa zaben da ya yi ko kuma ya bayyana fitar sa daga jam'iyyar APC.

Wasu masu nazarin siyasar jihar Legas sun bayyana cewar saboda sanin cewar Ambode zai fadi zaben cikin gida a APC ya saka jam'iyyar PDP ta daga nata zaben a jihar har sau biyu domin ko Ambode zai canja sheka idan ya fadi.

DUBA WANNAN: Ya mare shi, shi kuma ya cije shi: Hadiman Buhari biyu sun yi fada a kan zaben fitar da dan takarar gwamna a APC

Alamar cewar akwai kamshin gaskiya a wannan zargi ta fito fili ne bayan jam'iyyar PDP ta gaggauta fitar da sanarwar cewar gobe, Alhamis, 4 ga watan Oktoba zata gudanar da nata zaben jim kadan bayan Ambode ya kammala jawabinsa dake nuna zai cigaba a jam'iyyar APC duk da kasancewar bai samu tazarce ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel