Sabuwar nasara: Rundunar sojin sama ta tarwatsa mabuyar mayan Boko Haram a Borno

Sabuwar nasara: Rundunar sojin sama ta tarwatsa mabuyar mayan Boko Haram a Borno

- Rundunar sojin sama NAF ta ce ta samu nasarar lalata mabuyar mayakan Boko Haram da ke jihar Borno

- Rundunar ta yi amfani da jirgin yakin sama wajen kai harin, inda ta lalata mabuyar tare da kashe mayakan Boko Haram da dama

- Ta gano cewa akwai yawan mayakan Boko Haram a kwaryar Bula Korege da ke gabar dajin Sambisa

Rundunar sojin sama NAF ta ce ta samu nasarar lalata mabuyar mayakan Boko Haram da ke Kollaram da Bula Korege a jihar Borno, ta hanyar yin amfani da jiragen yakinta na sama inda suka yiwa mabuyar dirar mikiya a ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun rundunar sojin saman, AC Ibikunle Daramola ya ce a lokacin da rundunar atisayen dirar aradu ta 2 ta shiga cikin kwana na 5 a ranar 7 ga watan Satumba, 2018, dakarun sojin sama na ATF da ke atisayen Lafiya Dole ta sake samun nasarar tarwatsa mabuyar mayakan Boko Haram da ke yankin dajin Sambisa.

Ya ce rundunar ta kai wannan hari ga mabuyar mayakan Boko Haram dinne biyo bayan dogon bincike da sa ido a yankunan, tare da taimakon rahotanni daga jama'ar yankin, wanda ya taimaka ha suka gano mabuyar mayakan a yankunan guda biyu.

Sabuwar nasara: Rundunar sojin sama ta tarwatsa mabuyar mayan Boko Haram a Borno

Sabuwar nasara: Rundunar sojin sama ta tarwatsa mabuyar mayan Boko Haram a Borno
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Rundunar soji ta sake gano motoci 2 a cikin kududdufin Jos a kokarin neman wani Manjo-Janar

Ya bayyana cewa: "A fayyace, rundunar ATF ta yi amfani da jirgin yakin sama wajen kai hari a mabuyar, inda ta lalata mabuyar tare da kashe mayakan Boko Haram da dama."

"A ingantaccen bincike da leken asiri da rundunar ta gudanar a tsarin ISR, ta gano cewa akwai yawan mayakan Boko Haram a kwaryar Bula Korege da ke gabar dajin Sambisa, inda ta gano wasu gine gine da mayakan na BH ke amfani da su a matsayin mabuyarsu."

"Da wannan ne yasa rundunar ta NAF ta yi amfani da jirgin yakinta na Alpha Jet tare da wasu jiragejirage masu saukar Angulu guda biyu. Yanzu haka mayakan BH da suka tsira na guduwa daga yankuna, yayinda rundunar ta yi amfani da jirginta kirar Mi-35M wajen binsu da luguden harsasai," a cewar Ademola.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng HausSa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel