Yanzu-Yanzu: Ambode ya kira taron 'yan jarida, zaiyi wata muhimmiyar jawabi

Yanzu-Yanzu: Ambode ya kira taron 'yan jarida, zaiyi wata muhimmiyar jawabi

Bayan Ciyaman din jam'iyyar APC reshen jihar Legas ya sanar da cewar Babajide Sanwo-Olu ne ya lashe zaben cikin gida na masu neman takarar gwamna a jihar Legas a akayi a ranar Talata, gwamna mai ci Akinwunmi Ambode ya kira taron 'yan jarida inda ake sa ran zaiyi wasu bayanai masu alaka da zaben.

Mun samu daga shafin Sahara Reporters cewar gwamna Akinwunmi Ambode na jihar Legas zai yiwa al'ummar jihar jawabi a yau misalin karfe 2.30 na rana.

Wannan jawabin na zuwa ne bayan an sanar da cewa abokin hammayarsa na a zaben fidda gwani, Babajide Sanwo-Olu ya lashe tikitin takarar gwamna na jam'iyyar APC a akeyi zaben a ranar Talata a Legas.

Yanzu-Yanzu: Ambode ya kira taron 'yan jarida, zaiyi wata muhimmiyar jawabi

Yanzu-Yanzu: Ambode ya kira taron 'yan jarida, zaiyi wata muhimmiyar jawabi
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Dan Sule Lamido ya lashe takarar kujerar Sanata a PDP

Zaben yana dauke ta sarkakiya saboda Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar da farko ta ce ba'a gudanar da zaben fidda gwani a jihar ba, Ciyaman din jam'iyyar na reshen jihar Legas ya sanar da cewa Sanwo-Olu ne wanda ya lashe zaben cikin gidan.

Mafi yawancin 'yan jam'iyyar sun juyawa Ambode baya ne saboda shugaban jam'iyyar na kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nuna rashin gamsuwarsa da sake tsayawar Ambode inda ya ce baya tafiya tare da 'yan jam'iyya.

A bangarensa, Ambode ya yi ikirarin cewa Sanwo-Olu yana da tabuwar hankali saboda haka bai dace a mika masa tikitin takarar jam'iyyar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel