Rundunar soji ta sake gano motoci 2 a cikin kududdufin Jos a kokarin neman wani Manjo-Janar

Rundunar soji ta sake gano motoci 2 a cikin kududdufin Jos a kokarin neman wani Manjo-Janar

- Rundunar soji ta sake gano wasu motoci guda biyu daga tsohon tafkin da ke garin Lafendeg, gundumar Du

- Motar ta biyu na dauke da lambar Filato RYM 307 XA

- Manjo Janar Idris Alkali ya bace ne tun ranar 3 ga watan Satumba a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja

Rundunar soji ta sake gano wasu motoci guda biyu daga tsohon tafkin da ke garin Lafendeg, gundumar Du, da ke karamar hukumar Jos ta Kudu, jihar Filato, tafkin da a ranar asabar rundunar ta gano motar Manjo-Janar Idris Alkali da ya bace.

An tsamo motar Alkali kwanaki 9 bayan da hadakar jami'an soji da Manjo-Janar Tukur Buratai ya kafa suka soma yashe ruwan da ke cikin tafkin zuwa na kusa da shi don gano Manjo-Janar din kamar yadda aka yi zargin ko an jefa shi a ciki.

An bi sahun wayar salular Janar Alkali har zuwa gundumae Du ta hanyar amfani da na'urar gano inda waya take, wanda kuma rundunar sojin ta ce ta samu kwakkwaran rahoton cewa babban jami'in sojin da ya yi ritaya, ana zargin an kashe shi tare da jefa motarsa cikin tafkin Du.

KARANTA WANNAN: Tsawa ta kashe shanu 23 a jihar Ekiti

Rundunar soji ta sake gano motoci 2 a cikin tafkin Jos a kokarin neman wani Manjo-Janar

Rundunar soji ta sake gano motoci 2 a cikin tafkin Jos a kokarin neman wani Manjo-Janar
Source: Twitter

Sai dai, a kokarin da rundunar sojin ta yi tare da taimakon wasu masunta, sun gano Bas kirar Toyota da lambar Filato RYM 307 XA, wacce aka tsamo gaban Kwamandan Operation Safe Haven, Manjo-Janar Augustine Adundu, tare da babban jami'in da ke kula da runduna ta 3 a rundunar ta Rukuba, Manjo-Janar Benson Akinruluyo da kuma manema labarai

A ranar Asabar ne Legit.ng ta kawo maku rahoton cewar hukumar sojin Najeriya ta gano motar Janar (mai ritaya) a karkashin wani kududdufi dake unguwar Dura Du a karamar hukumar Jos ta kudu, bayan fiye da sati uku ana nemansa.

Manjo Janar Idris Alkali ya bace ne tun ranar 3 ga watan Satumba a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja. Rahotannin da hukumar soji ta tattara sun gano cewar Alkali ya bata ne a karamar hukumar Jos ta kudu.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel