Hukumar yaki da rashawa ta tasa keyar Dakingari har gaban kan satar N1, 094, 320,000

Hukumar yaki da rashawa ta tasa keyar Dakingari har gaban kan satar N1, 094, 320,000

Hukumar yaki da rashawa da sauran makamantan ayyuka, ICPC ta tasa keyar tshon gwamnan jahar Kebbi, Saidu Nasamu Dakingari zuwa gaban wata babbar kotun jahar Kebbi dake zamanta a garin Birnin Kebbi kan zarginsa da handamar kudi naira 1, 094, 320, 000 mallakin jahar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ICPC na zargin gwamnan ne da hada baki da kwamishinan kudi na jahar, Mohammed Tunga da sakataren gwamnatin jahar, Garba Kamba inda suka kwashe naira N349, 475, 000 da nufin sayen janareta da sauran kayan aiki ga duk akwatin zabe dake jahar a zabukan 2015.

KU KARANTA: Yansanda sun binciko muggan makamai guda 819 da bindigogu 45 a jahar Kano

Sai dai a zaman na ranar Laraba an sanar da kotu cewar guda daga cikin wadanda ake tuhumar, wato tsohon kwamishinan kudin jahar, Mohammed Tunga ya rasu, don haka lauyan ICPC ya bukaci kotu ta soke sunansa daga cikin wadanda take kara.

Lauya Elija Akahol ya cigaba da karanto tuhume tuhumen da suka yi ma Dakingari, inda yace tsohon gwamnan ya barnatar da makudan kudade da suka kai N430, 000, 000 tare da abokansa da sunan zasu tallafa ma jami’an tsaro da kudaden aiki a yayin zaben 2015.

Haka zalika ana tuhumar Dakingari da zaftare naira miliyan 315 daga baitil malin gwamnatin da sunan zai baiwa Malamai kudaden don su wayar da kawunan al’umma game da muhimmancin zaben 2015 a kananan hukumomi 21.

Daga karshe ICPC ta jero tuhume tuhume guda shida da take yi ma Dakingari da duka shafi hada kai wajen aikata miyagun laifuka, sata, yi ma abokai alfarmada rashawa da kuma amfani da mukami don satar kudi.

Sai dai Dakingari ya musanta dukkanin tuhume tuhumen a gaban Alkali, daga nan sai lauyansa, Adegboyega Awomolo ya bukaci kotu ta bada belin wanda yake karewa ta cikin wata rubutacciyar wasika, inda Alkali ya bada belinsa akan N30m, sa’annan ya dage karar zuwa 4 ga watan Disamba

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel