Ajimobi ya lashe zaben fidda gwanin takarar Kujerar Sanatan Oyo ta Kudu

Ajimobi ya lashe zaben fidda gwanin takarar Kujerar Sanatan Oyo ta Kudu

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, ya yi babbar nasara ta lashe tikitin takara na jam'iyyar APC yayin zaben fidda gwanin takarar kujerar sanatan jihar ta Kudu da aka gudanar a jiya Talata.

Baturen Zaben Cif Ademola Seriki, shine ya bayyana hakan da cewar Ajimobi wanda ya samu kuri'u 2,659 ya lallasa abokin takararsa, Dakta Fola Akinosun, da ya tashi da kuri'u 168 kacal.

Ajimobi na sake hankoron komawa kujerar majalisar dattawa bayan ya wakilci jiharsa ta Oyo a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007 karkashin jam'iyyar AD, Alliance for Democracy.

Cif Ademola a yayin bayyana sakamakon zaben da sanyin safiyar yau ta Laraba ya bayyana cewa, an fara gudanar da zaben ne da misalin karfe 6.30 na yammacin ranar Talatar da ta gabata a sakamakon tsaikon kawo kayayyakin zaben daga babban ofishin jam'iyyar dake birnin tarayya na Abuja.

Ajimobi ya lashe zaben fidda gwanin takarar Kujerar Sanatan Oyo ta Kudu

Ajimobi ya lashe zaben fidda gwanin takarar Kujerar Sanatan Oyo ta Kudu
Source: Depositphotos

Kujerar Sanatan Oyo ta Kudu ta hadar da kananan hukumomi 9 na jihar da suka hadar da; Ibarapa ta Arewa, Ibarapa ta Gabas, Ibarapa ta Tsakiya, Ido, Ibadan ta Arewa, Ibadan ta Kudu maso Gabas, Ibadan ta Kudu maso Yamma, Ibadan ta Arewa maso Gabas da kuma Ibadan ta Arewa maso Yamma.

KARANTA KUMA: Abinda na shaidawa Buhari kan Zaben fidda gwani na jihar Legas - Oshiomhole

Sai dai Sanata mai rike da wannan kujera a majalisar dattawa, Mista Soji Akanbi, bai sake neman kujerar ta sa saboda wasu da dalilai da manema labarai ba su samu damar kai wa gare su ba.

A yayin ganawarsa da manema labarai bayan nasarar lashe tikitin takara, Gwamna Ajimobi ya yabawa kwamitin zaben da suka gudanar da shi cikin lumana kuma ba tare da bata wani lokaci ba.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, an yankewa wata Budurwa hukuncin kisa ta hanyar rataya can kasar Iran bayan ta hallaka Mijinta da a cewarta ya saba munzguna rayuwarta.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel