Tsawa ta kashe shanu 23 a jihar Ekiti

Tsawa ta kashe shanu 23 a jihar Ekiti

- Bayan tafka ruwa kamar da bakin kwarya, tsawa ta kashe shanu 23 a jihar Ekiti

- Abdullahi Kadiri ya ce ya isa gonar bayan awanni 6 da dauke ruwan ya taras da gawarwakin shanun ba tare da wani rauni a jikinsu ba

- Shugaban yankin, Chief Joseph ya roki masu hannu-da-shuni a yankin da su taffawa Kadiri don farfado da kasuwancinsa

Tsananin rugudin aradu da walkiya mai tsanani ta haddasa tsawa mai karfi a ranar Talata, wanda ta sauka a cikin gungun wasu shanu a Okeowa Eluju, wata gona da ke garin Iloro-Ekiti, karamar hukumar Ijero da ke jihar Ekiti, tare da kashe shanu 23.

Tsawar wacce ta biyo bayan wani ruwa da aka tafka kamar da bakin kwarya a yankin, ya jawo jama'a shiga yanayin tsoro-tsoro da dimaucewa. Wani makiyayi, Abdullahi Kadiri, ya bayyana wannan iftila'i a matsayin bakon al'amari a garesu.

Da ya ke labartawa manema labarai yadda al'amarin ya faru, Abdullahi ya ce, "Na isa gonar da misalin awanni 6 bayan daukewar ruwan da aka tafka kamar da bakin kwarya a ranar Litin, sai na taras da shanu 23 a kwance sun mutu."

Tsawa ta kashe shanu 23 a jihar Ekiti

Tsawa ta kashe shanu 23 a jihar Ekiti
Source: UGC

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Buhari ya lalata Nigeria fiye da tunanin mutane - Gwamna Fayose

Ya ce: "Duk da cewar sun mutu, amma babu wata alama ta cewar sunji raunuka a jikinsu. Ina da yakinin cewa wannan iftila'i ne daga Allah, tunda na san cewa bana gaba ko fada da kowa balle na yi zaton wani ne ya aikata hakan a gare ni."

Kadiri wanda ya bayyana cewa shi dan gado ne a harkar kiwon dabbobi, ya kuma ce bai taba fuskantr irin wannan iftila'in ba tsawon shekaru 35 da ya kwashe yana harkar.

Shugaban garin, Chief Joseph Alofe ya bayyana Kadiri a matsayin mutum mai dattako da son zaman lafiya musamman a harkar kasuwancinsa ta kiwon dabbobi da sayar da su.

Chief Joseph ya kuma bayyana wannan iftila'in a matsayin bakon abu a garesu, tare da yin kira ga masu hannu-da-shuni da ke a yankin, da su tallafawa makiyayain don farfado da kasuwancin sa.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel