Gwamnatin Tarayya naso ta kai kudin makarantu na jami'a N350,000 - inji ASUU

Gwamnatin Tarayya naso ta kai kudin makarantu na jami'a N350,000 - inji ASUU

- Kakakin ASUU na jami'o'i yace gwamnati na so ta kara kudin makarantu

- Ministan ilimi bai mayar da martani ba

- An sha tafka yajin aiki a baya

Gwamnatin Tarayya naso ta kai kudin makarantu na jami'a N350,000 - inji ASUU

Gwamnatin Tarayya naso ta kai kudin makarantu na jami'a N350,000 - inji ASUU
Source: Facebook

ASUU, kungiyar malaman makarantun gaba da sakandare ta kasa a jami'o'in kasar nan, ta shafe shekaru kusan 40 tana gwara wa da gwamnati, a yaje-yajen aiki don neman gwamnati ta baiwa ilimin boko kulawar da ta kamata.

A wannan karon, bayan da aka ito daga dakin sulhu, ASUU ta tona yadda gwamnatin APC ke kokarin maida karatun boko na kudi tsababa.

Dama ko a hakan dai ba kowa ke samun ilimin ba balle ma ace wai kuma an maida kudin kusan rabin miliyan na naira.

DUBA WANNAN: Zunubin Ambode

Dr. Ade Adejumo, mai kula da ofishin kungiyar na shiyyar yamma a kudancin Najeriya, shi ya bayyana hakan inda yace bayan zantawarsu da gwamnati a lokacin sulhun yajin aikin kwadago ne gwamnatin tarayyar ta fadi haka.

A cewarsa; "karin kudin makaranta zuwa N350,000 zai ruguza tsarin kwadago na jami'ar, kuma wannan dalilin ne yasa muka ice daga yarjejeniyar da muke kai a wannan karon."

Ya kara bayani da cewa, dole ce tasa in bayyana wa duniya wannan tuggu, inda wai gwamnati zata kafa bankuna da zasu baiwa dalibai bashi don kammala karatun, daga baya su biya, kamar yadda dai ake a kasashen da suka riga suka ci gaba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel