Zunubinsa: Ambode ya iya aiki, amma bai tafi da jama'armu ba a siyasa - Tinumbu

Zunubinsa: Ambode ya iya aiki, amma bai tafi da jama'armu ba a siyasa - Tinumbu

- Duk da dai Ambode yayi kokari a ofishin shi, amma bai iya siyasa ba

- Jam'iyyar ta yanke shawarar janye goyon bayan shi, duk da yaso zarcewa

- Ba wai son raina nabi ba, umarnin mutane nabi

Zunubinsa: Ambode ya iya aiki, amma bai tafi da jama'armu ba a siyasa - Tinumbu

Zunubinsa: Ambode ya iya aiki, amma bai tafi da jama'armu ba a siyasa - Tinumbu
Source: UGC

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar talata yace, duk da gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode yayi kokari a ofishin shi, amma bai iya siyasa ba.

A saboda wannan dalilin ne jam'iyyar APC ta yanke shawarar janye goyon bayan shi na zarcewa.

Ya jaddada cewa maye gurbin Ambode da Babajide Sanwo-Olu ba ra'ayin shi bane. Ya kara da cewa yayi hakan ne don cika burin jam'iyya, wadanda sune suka bashi jagoranci.

Tinubu yayi maganar ne da yan jaridu a ward C, karamar hukumar Ikeja, bayan yanke hukuncin zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Legas.

DUBA WANNAN: Ambode bashi da karfi a APC - Tinubu

Da aka tambaye shi dalilin janye goyon bayan Ambode, Tinubu yace, "Wa nake goyon baya a 2014? Ambode ne. Rayuwa fadi gareta. Wadanda suka sani jagoranci ne suka nuna min ga abinda suke so. Sai kana da mabiya ne kake zama shugaba a damokaradiyya. Idan ka waiwaya kaga babu su, toh ka tashi daga shugaba. Idan bana biya musu bukatun su, toh bazan ci Jarabawar shugabancin ba."

Ya Kwatanta zaben fidda gwanin na Kato bayan Kato a matsayin cigaban damokaradiyya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel