Abinda na shaidawa Buhari kan Zaben fidda gwani na jihar Legas - Oshiomhole

Abinda na shaidawa Buhari kan Zaben fidda gwani na jihar Legas - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya zayyana abinda ya shaidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnatin jihar Legas da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata.

A yayin da ake ci gaba kai ruwa rana dangane da zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnatin jihar Legas a karkashin jam'iyyar APC, Oshiomhole ya bayyana cewa tuni shugabancin jam'iyyar ya tunkari lamarin tare da gano bakin zaren dambarwar da ta mamaye siyasar jihar.

Oshiomhole kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito ya bayyana hakan ne cikin babban birnin kasar nan na tarayya yayin amsa tambayoyin manema labarai dangane da sakamakon zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar a jihar ta Legas.

Abinda na shaidawa Buhari kan Zaben fidda gwani na jihar Legas - Oshiomhole

Abinda na shaidawa Buhari kan Zaben fidda gwani na jihar Legas - Oshiomhole
Source: Depositphotos

Shugaban jam'iyyar ya bayar da shaidar hakan ne ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaba Buhar, inda ya ce shugabancin jam'iyyar yana da masaniya tare da tunkarar al'amurran da suka shafi zaben fidda gwani na jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Kasar Denmark za ta hana amfani da Motoci masu amfani da Man fetur da makamashin gas

Dangane da abinda ya shaidawa shugaba Buhari yayin ganawarsu, Oshiomhole ya tabbatarwa da shugaban kasar cewa ba bu gudu ba bu ja da baya dangane da salon zaben 'yar tinke da za a dabbaka yayin zaben fidda gwani a jihar ta Legas.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugabancin jam'iyyar PDP reshen jihar Kano ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnan jihar da aka gudanar cikin daular Kwankwasiyya a jiya Talata.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel