Daga karshe: An umurci jami'an tsaro su kawo karshen rikicin jihar Filato da gaugawa

Daga karshe: An umurci jami'an tsaro su kawo karshen rikicin jihar Filato da gaugawa

- An umurci jami'an tsaro su kawo karshen rikicin jihar Filato da gaugawa

- Ministan harkokin cikin gida Dambazau ya yi wannan umurnin

- Yace kuma suma 'yan jihar dole ne su rungumi zaman lafiya

Babban ministan harkokin cikin gida kuma mamba a majalisar zartarwar shugaba Buhari, Laftanal Janar Abdulrahman Dambazau ya umurci jami'an tsaron kasar nan da su lalubo hanyoyin da suka dace domin kawo karshen rikicin jihar Filato.

Daga karshe: An umurci jami'an tsaro su kawo karshen rikicin jihar Filato da gaugawa

Daga karshe: An umurci jami'an tsaro su kawo karshen rikicin jihar Filato da gaugawa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An gano babban dakin taron 'yan kungiyar Boko Haram

Dambazau, wanda ya nuna jimamin sa da da rashin jin dadi game da yadda rikicin na jihar kan lakume rayuka da dukiyoyi a duk lokacin da ya auku, ya ce dole ne a kawo karshen sa cikin gaugawa.

Legit.ng ta samu cewa a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar dauke da sa hannun babban jami'in sa na yada labarai, Mista Ehisienmen Osaigbovo, ya kara da cewa dole ne jami'an tsaron kasar su kara kaimi wajen kokarin da suke yi domin ganin an magance dukkan wani hatsabibi dake son kawo hatsaniya.

Haka kuma Ministan ya ja hankalin 'yan jihar ta Filato da su rungumi zaman lafiya domin samun cigaba mai dorewa.

A wani labarin kuma, Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a wajen taron bukukuwan cikar Najeriya shekaru 58 da samun 'yancin kai ya tsokani Sanatocin jam'iyyar adawa ta PDP biyu sadda yake jawabin sa.

Wadanda mataimakin shugaban kasar ya tsokana dai sun hada da Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi sai kuma Sanata Adeleke Ademola da ke zaman dan takarar kujerar gwamna a zaben da aka gudanar jihar Osun kwanan baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel