Mataimakin shugaban kasa a tsokani Dino Melaye, da Adeleke a wajen taro

Mataimakin shugaban kasa a tsokani Dino Melaye, da Adeleke a wajen taro

- Mataimakin shugaban kasa a tsokani Dino Melaye, da Adeleke a wajen taro

- Yace yan Najeriya mutane ne masu tsantsar farinciki

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a wajen taron bukukuwan cikar Najeriya shekaru 58 da samun 'yancin kai ya tsokani Sanatocin jam'iyyar adawa ta PDP biyu sadda yake jawabin sa.

Mataimakin shugaban kasa a tsokani Dino Melaye, da Adeleke a wajen taro

Mataimakin shugaban kasa a tsokani Dino Melaye, da Adeleke a wajen taro

KU KARANTA: An gano wani gwamnan APC da bai yi NYSC ba

Wadanda mataimakin shugaban kasar ya tsokana dai sun hada da Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi sai kuma Sanata Adeleke Ademola da ke zaman dan takarar kujerar gwamna a zaben da aka gudanar jihar Osun kwanan baya.

Legit.ng ta samu cewa Osinbajo, wanda yace tabbas mutanen Najeriya na daya daga cikin al'ummomin duniya da ke cikin farin ciki da annashuwa inda ya bayyana fitattun 'yan siyasar a matsayin daya daga cikin masu sa 'yan kasar farin ciki.

Osinbajo ya ce: "A lokacin baya akwai wani Sanata da yace an sace shi amma ya samu ya kubuta har ma ya shafe kusan sama da awa 11 a saman icce sannan kuma akwai wani Sanatan da kware wajen rawa kuma duk inda yaje ba abun da yake yi sai rawa amma dukan su suna da magoya baya a Najeriya.

A wani labarin kuma, Babban ministan harkokin cikin gida kuma mamba a majalisar zartarwar shugaba Buhari, Laftanal Janar Abdulrahman Dambazau ya umurci jami'an tsaron kasar nan da su lalubo hanyoyin da suka dace domin kawo karshen rikicin jihar Filato.

Dambazau, wanda ya nuna jimamin sa da da rashin jin dadi game da yadda rikicin na jihar kan lakume rayuka da dukiyoyi a duk lokacin da ya auku, ya ce dole ne a kawo karshen sa cikin gaugawa.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewarku tare da mu

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel