Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari na shirin maida kudin karatun jami'a Naira 350,000

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari na shirin maida kudin karatun jami'a Naira 350,000

- Gwamnatin Buhari na shirin maida kudin karatun jami'a Naira 350,000

- Kungiyar ASUU ce ta yi zargin hakan

- Kungiyar ta bukaci yan Najeriya su tashi tsaye su hana hakan

Shugabannin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya watau Academic Staff Union of Universities, (ASUU) a takaice ta zargi cewa gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari na shirin mayar da kudin karatun jami'a ya zuwa Naira budu dari 350.

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari na shirin maida kudin karatun jami'a Naira 350,000

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari na shirin maida kudin karatun jami'a Naira 350,000
Source: Facebook

KU KARANTA: Manyan matsafa 13 daga Arewa sun shiga hannun jami'an tsaro

Wannan zargin dai ya fito ne daga bakin shugabannin kungiyar na shiyyar Kudu maso gabashin kasar nan a lokacin da suke zantawa da manema labarai a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Legit.ng ta samu cewa da yake maida jawabi a gaban 'yan jaridar, shugaban kungiyar a matakin shiyya, Dakta Ade Adejumo ya kuma bukaci 'yan Najeriya da su tashi tsaye su yaki wannan kudurin na gwamnati domin basu damar bayar da ilimi cikin sauki ga 'yan Najeriya.

Mai karatu dai idan bai manta ba kungiyar ta malaman jami'a tuni suke ta rade-raden za su sake komawa yajin aiki muddun gwamnati bata cika masu alkawurran da ta daukar masu ba.

A wani labarin kuma, Wani dan majalisar wakilai a zauren majalisar taraya dake wakiltar mazabar Taura da Ringim a jihar Jigawa dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, Muhammad Gausu Boyi ya sha da kyar a hannun wasu mafusatan matasa.

Kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu, lamarin dai ya faru ne a garin Dutse dake zaman babban birnin jihar inda dan majalisar tare da wasu magoya bayan sa suka je domin tantance su a gabanin zabukan fitar da gwani da za'a gudanar.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewarku tare da mu

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel