Zaben fidda gwani na APC: Gulak yayi Allah wadai da soke zaben Imo

Zaben fidda gwani na APC: Gulak yayi Allah wadai da soke zaben Imo

Shugaban kwamitin zaben fidda gwanin gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Imo, Ahmed Gulak yayi Allah wadai da soke zaben.

Ya bayyana cewa zaben fidda gwani da ya gudana a ranar Talata, 2 ga watan Oktoba ya kammalu kuma cewa roko shine hanya guda da aka bude ma wadanda ke fafutuka.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Mista Adams Oshiomhole ya soki sakamakon zaben inda ya bayyana shi a matsayin na bogi.

Zaben fidda gwani na APC: Gulak yayi Allah wadai da soke zaben Imo

Zaben fidda gwani na APC: Gulak yayi Allah wadai da soke zaben Imo
Source: UGC

Don haka, ya dakatar da kwamitin wanda Gulak ke jagoranta wanda sune suka gudanar da zaben fidda gwanin, inda ya bayyana cewa za’a kafa wata kwamiti nan take domin gudanar da sabon zaben fidda gwani.

Don haka Gulak ya bayyana cewa lallai sabanin hukuncin shugaban jam’iyyar, kwamitinsa sunyi yadda ya kamata kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya koka kan yadda ake kashe rayukan bayin Allah a Jos

A baya Legit.ng ta rahotyo cewa biyu daga cikin sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dake mulki a jihar Niger sun fadi zaben fidda gwani a kokarinsu na ganin sun koma majalisar dokokin kasar a ranar Talata, 2 ga watan Satumba.

Sanatocin biyu sun sha kaye ne a zaben fidda gwani da aka gudanar a fadin yankuna uku na jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel