Shugaban PDP a Kano ya koka da dawowar ‘Yan Kwankwasiyya cikin Jam’iyya

Shugaban PDP a Kano ya koka da dawowar ‘Yan Kwankwasiyya cikin Jam’iyya

Mun samu labari cewa masu neman takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar PDP sun yi watsi da sakamakon zaben fitar da gwani wanda aka yi kwanan nan inda su kace ba fa zabe aka yi ba.

Shugaban PDP a Kano ya koka da dawowar ‘Yan Kwankwasiyya cikin Jam’iyya

Salihu Sagir Takai bai yarda da zaben da PDP tayi a gidan Kwankwaso ba
Source: Depositphotos

Kamar yadda mu ka samu labari ‘Yan takaran PDP sun nuna cewa taron Kwankwasiyya kurum aka yi ba zaben fitar da gwani ba. Wasu masu neman takara a PDP sun bayyana cewa idan ba a kawo dauki ba, lallai za su bar PDP.

Malam Salihu Sagir Takai wanda yana cikin masu neman Gwamnan a PDP yace bai san da zaman zaben da ‘Yan Kwankwasiyya su kayi ba. Takai ya bayyana wannan ne ta bakin Mai magana da yawun sa watau Auwal S. Muazu.

KU KARANTA: Kaduna ta rikice bayan APC ta ba Shehu Sani tikitin Sanata a sama

An dai gudanar da zaben ne a cikin dare a gidan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda hakan ta sa Ibrahim Little wanda yana cikin ‘Yan takarar Gwamna a PDP yace sam ba a bi ka’ida wajen gudanar da zaben ba.

Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda Suruki ne wajen tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ne yayi nasara a zaben takarar Gwamna. Shugaban PDP a Jihar Mas’ud El-Jibril Doguwa yace wala-wala kurum ‘Yan Kwankwasiyya su kayi ba zabe ba.

Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa yace idan har PDP ba tayi abin da ya dace ba lallai za su sauya-sheka ba da dadewa ba. Doguwa ya soki zaben da aka yi inda yace dawowar su Kwankwaso PDP bai zo wa Jam’iyyar da alheri a Jihar Kano ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel