2019: Dino Melaye yayi nasara a zaben fitar da gwani na PDP

2019: Dino Melaye yayi nasara a zaben fitar da gwani na PDP

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa da aka dai je da aka dawo, Sanata Dino Melaye zai sai sake takarar Sanata a zabe mai zuwa 2019 bayan ya lashe zaben fitar da gwani da aka ayi Jam’iyyar PDP.

2019: Dino Melaye yayi nasara a zaben fitar da gwani na PDP

Dino ya lashe tikitin Jam’iyyar adawa na PDP. na Sanatan Kogi
Source: Depositphotos

Jam’iyyar PDP ta tsaida Dino Melaye a matsayin ‘Dan takarar ta na Majalisar Dattawa wanda zai wakilci Yankin Kogi ta Yamma a 2019. Babban Jami’in da ya gudanar da zaben fitar da gwanin watau Jude Sule ya tabbatar da wannan.

An yi zaben ne a wani otel da ke Garin Kabba wanda nan ne Hedikwatar Yankin na Yammacin Jihar Kogi. Sule ya tabbatar da cewa Dino Melaye ya samu kuri’u fite da 800 daga Kananan Hukumomi 7 da ake da su a Yankin Jihar.

KU KARANTA: Sanata Shehu Sani ya samu tikitin APC a sama a Jihar Kaduna

Sai dai an nemi ayi rigima wajen zaben domin kuwa sai da Jam’iyyar adawar Kasar ta haramtawa wasu masu neman kujerar takara inda wasu kuma su ka janyewa Sanatan. Melaye dai yace bai yi mamakin nasarar da ya samu a PDP ba.

Wani ‘Dan Majalisar Tarayya Sunday Karimi, da kuma tsohon Kakakin Majalisar dokokin Jihar Clement Olafemi da Hon. Henry Ojuola, da Hon. Oreniya Salaudeen su na cikin wadanda aka hana takara da Dino Melaye a Jam’iyyar PDP.

A Yankin Kogi ta tsakiya ma dai ana sa rai cewa Sanata Ahmed Ogembe ne jam’iyyar PDP za ta tsaida. Sanata Ogembe dai kamar Dino Melaye, shi ne ke rike da kujerar a Majalisar Dattawa yanzu haka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel