Yansanda sun binciko muggan makamai guda 819 da bindigogu 45 a jahar Kano

Yansanda sun binciko muggan makamai guda 819 da bindigogu 45 a jahar Kano

Rundunar Yansandan jahar Kano ta sanar da kwato tarin makamai daga hannun jama’a a jahar Kano da suka hada da bindigogi guda arba’in da biyar da sauran muggan makamai dari takwas da goma sha tara, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rudunar Yansandan jahar, SP Magaji Musa Majia ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da manema labaru a garin Kano, inda yace daga cikin makaman da suka gano har da alburusai dubu da dari daya da goma sha bakwai.

KU KARANTA: Sulhu alheri ne: An sasanta tsakanin yan takarar gwamna da zasu fafata a zaben fidda gwani a Zamfara

Yansanda sun binciko muggan makamai guda 819 da bindigogu 45 a jahar Kano

Bindigu
Source: Twitter

Maia yace rundunar ta yi wannan kamenne a tsakanin watan Janairu zuwa Agustan shekarar 2018, sa’annan yace an gudanar da wannan aikin ne bisa umarnin babban sufetan yansandan Najeriya, IG Ibrahim Idris.

“A sakamakon samame daban daban da rundunar Yansandan jahar ta kai da kama manyan yan fashi da makami, rundunar Yansandn jahar Kano ta kwato bindigu 45, miyagun makamai 819 da alburusai 1, 117 daga Janairu zuwa Agusta.

“Zamu cigaba da aikin kwace makamai daga hannun duk wasu miyagun mutane tare da kakkabe yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane daga jahar gaba daya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, an samu takaddama tsakanin yayan kungiyar Kwankwasiyya na jam’iyyar PDP da rundunar Yansandan jahar Kano bayan Yansandan sun garkame Marhaba silma inda PDP ta shirya gudanar da zaben fidda gwanin da zai tsaya mata takara a zaben 2019.

Wannan matakin da Yansanda suka dauka ya tursasa ma yayan jam’iyyar PDP garzayawa gidan jagoran kwankwasiyya, kuma tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda aka gudanar da wannan zabe, kuma surukin Kwankwaso, Abba Yusuf ya lashe zaben.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel