Da duminsa: Babajide Sanwo-Olu ne ya lashe zaben fidda gwani a Legas

Da duminsa: Babajide Sanwo-Olu ne ya lashe zaben fidda gwani a Legas

Jam'iyyar APC reshen jihar Legas ta sanar da cewar Babajide Sanwo-Olu ne wanda ya yi nasara a zaben fidda gwani na takarar kujerar gwamna a jihar a zaben 2019.

Ciyaman din jam'iyyar, Tunde Balogun ne ya bayar da sanarwan ranar Talata, 2 ga watan Oktoba a Sakatariyar jam'iyyar da ke Legas.

A cewarsa, Sanwo - Olu ya samu kuri'u 970,851 yayin da gwamni mai ci yanzu, Akinwunmi Ambode ya samu kuri'u 72,901 a zaben.

DUBA WANNAN: Amsar da Buhari ya bawa wata kasa da ta nemi taimakon Najeriya wajen warware matsalolin ta

Wannan sanarwar tana zuwa ne bayan kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar ta soke zaben da aka gudanar.

A baya, Legit.ng ta ruwaito muku cea shugaban jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu yace gwamna Ambode ya yi bajinta a matsayinsa na gwamna amma baya tafiya tare da 'yan jam'iyya.

Ana ganin wannan dalilin ne yasa Asiwaju Bola Tinubu ya juyawa Akinwunmi Ambode baya a yunkurinsa na yin tazarce a jihar. Tinubu ya bayyana a fili cewar yana goyon bayan Babajide Sanwo-Olu ne wadda galibin 'yan majalisar jihar suma sun mara masa baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel