2019: Kungiyar Kiristoci za ta tura masu sa-ido 300 a zabe mai zuwa

2019: Kungiyar Kiristoci za ta tura masu sa-ido 300 a zabe mai zuwa

Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), Samson Ayokunle, ya bayyana cewa kungiyar su za ta kammala shirin yi wa kiristoci 300 taron bita da kuma bayar da horo, wanda za su yi domin aikin sa-ido su ga yadda za a gudanar da zaben 2019 a fadin kasar nan.

Ya yi wannan jawabi ne a wurin wani taron Kiristoci da aka gudanar a Lagas a ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba.

Samson yace za’a hado masu sa-idon ne daga kowace sashe na shiyyoyin kasar nan, inda horaswar da za a yi musu za ta ci kudi har naira miliyan 12.

2019: Kungiyar Kiristoci za ta tura masu sa-ido 300 a zabe mai zuwa

2019: Kungiyar Kiristoci za ta tura masu sa-ido 300 a zabe mai zuwa
Source: Depositphotos

Ya kara da cewa kungiyar su a shirye ta ke ta yi aiki kafada da kafada da kungiyar Musulmi, domin shata abubuwan da ake hasashen dan takara zai iya kasancewa ya na da su, da kuma abin da zai kara kawo hadin kai wajen gudanar da sahihin zabe.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tabbatar da Sanata Dino Melaye a matsayin dan takarar tan a sanata a yankin Kogi ta yamma a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya sallami kwamitin Gulak kan zaben fidda gwani na APC a Imo

An gudanar da zaben fitar da dan takara ne a Prestige Hotel dake Kabba, hedkwatar yankin.

Shugaban zaben, Mista Jude Sule yace Melaye ya lashe dukkanin kuri’un 800 harda na wakilai daga yankuna bakwai dake mazabar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel