2019: Daga Karshe PDP ta sallama wa Dino tikitin takarar kujeran Sanata a Kogi

2019: Daga Karshe PDP ta sallama wa Dino tikitin takarar kujeran Sanata a Kogi

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tabbatar da Sanata Dino Melaye a matsayin dan takarar tan a sanata a yankin Kogi ta yamma a zaben 2019.

An gudanar da zaben fitar da dan takara ne a Prestige Hotel dake Kabba, hedkwatar yankin.

Shugaban zaben, Mista Jude Sule yace Melaye ya lashe dukkanin kuri’un 800 harda na wakilai daga yankuna bakwai dake mazabar.

2019: Daga Karshe PDP ta sallama wa Dino tikitin takarar kujeran Sanata a Kogi

2019: Daga Karshe PDP ta sallama wa Dino tikitin takarar kujeran Sanata a Kogi
Source: Depositphotos

Zaben wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali ya samu kula daga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da wasu jami’an tsaro.

KU KARANTA KUMA: An matsawa yan takara lamba don su janyewa surikin Buhari

A halin da ake ciki, tabbatar da Dino Melaye ya zo da wasu lauje a cikin nadi domin kwamitin tantancewa na jam’iyyar sun ki tantance yan takara hudu yayinda wasu biyu suka janye masa hakan yasa ya zama bai da abokin adawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel