Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya sallami kwamitin Gulak kan zaben fidda gwani na APC a Imo

Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya sallami kwamitin Gulak kan zaben fidda gwani na APC a Imo

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Adams Oshiomhole a ranar Talata, 2 ga watan Oktoba yace jam’iyyar ta sallami kwamitin da Ahmed Gulak ke jagoranta na zaben fidda gwanin jam’iyyar na gwamna a jihar Imo.

Oshiomhole ya fadi hakan ne a wata hira da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawar da yayi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya sallami kwamitin Gulak kan zaben fidda gwani na APC a Imo

Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya sallami kwamitin Gulak kan zaben fidda gwani na APC a Imo
Source: Depositphotos

Tsohon gwamnan na jihar Edon wanda ya ce ya je fadar Villa ne don tuntubar Buhari kan cigaban da aka samu a zaben fidda gwani, yace sakamakon zaben fidda gwani na gwamnan jihar Imo ya kasance na jabu, don haka akwai bukatar korar kwamitin.

Ya bayyana cewa ana sanya ran za’a kammala tsarin kafin karshen mako.

A halin da ake ciki, mun ji cewa Uwar jam’iyyar APC ta watsa ma gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai kasa a idanu game da takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya da yake muradin hadiminsa Uba Sani ya tsaya don ya fafata da Shehu Sani, sanata mai ci.

KU KARANTA KUMA: An matsawa yan takara lamba don su janyewa surikin Buhari

Legit.ng ta ruwaito a ranar Talata 2 ga watan Oktoba ne aka shirya gudanar da zaben fitar da gwani na yan takarar Sanatocin jam’iyyar APC a jahar Kaduna, sai dai zaben bai yiwu ba sakamakon matsalar da aka samu game da jerin sunayen yan takarar da jam’iyyar APC da uwar jam’iyyar ta fitar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel