Wuta ta babbaka ofisoshin malamai 30 da sakamakon jarabawar dalibai a kwalejin kimiyya da fasaha

Wuta ta babbaka ofisoshin malamai 30 da sakamakon jarabawar dalibai a kwalejin kimiyya da fasaha

Akalla ofisoshin malamai guda talatin ne suka babbake a yayin da wata mummunar gobara ta tashi a kwalejin kimiyya da fasaha na Waziri Umaru Faruk Federal Polyetechni dake birnin Kebbin jahar Kebbi.

Legit.ng ta ruwaito gobarar ta tashi ne da misalin karfe daya na daren Talata 2 ga watan Satumba, a sanadiyyar wasu wayoyin wutar lantarki da suka hade a daya daga cikin ofisoshin malaman kwalejin.

KU KARANTA: Uwar jam’iyyar APC ta yi fatali da aminin El-Rufai daga takarar Sanata

Wuta ta babbaka ofisoshin malamai 30 da sakamakon jarabawar dalibai a kwalejin kimiyya da fasaha

Gobara
Source: Facebook

Sai dai ko kafin jami’an hukumar kashe wuta su farga, tuni wutar ta shiga har farfajiyar makarantar, kamar yadda kaakakin hukumar kashe wuta ta jahar Kebbi, Nasir Guru ya tabbatar.

Nasir yace sun samu rahoton tashin wutar tun da misalin karfe goma na safiyar ranar Talata, amma saboda karancin isassun kayan aiki basu samu damar kashe wutar da wuri ba, har sai bayan ya yi barna sosai.

Da yake tsokaci game da gobarar, shugaban kwalejin,Sani Aliyu yace “Bamu taba tsammanin irin wannan gobarar ba, amma a yanzu ba zan iya tabbatar da adadin barnar da ta yi da kuma asarar da ta janyo mana a yanzu ba.

“Abinda muka sani shine babban ofishin kwalejin yak one kurmus, haka zalika dakunan gwaje gwaje da dama sun babbake, sakamakon jarabawar dalibai da aka shirya ma duk sun kone, da kuma wasu muhimman takardu na kwalejin ilimin kimiyya da fasaha.” Inji shi.

Shima gwamnan jahar Kebbi Atiku Bagudu ya jajanta ma shuwagabanni da daliban kwalejin a wata ziyarar ba zata da ya kai makaranta, inda yayi alkawarin bada gudunmuwa don ganin makarantar ta farfado.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel