Kasar Denmark za ta hana amfani da Motoci masu amfani da Man fetur da makamashin gas

Kasar Denmark za ta hana amfani da Motoci masu amfani da Man fetur da makamashin gas

Mun samu cewa kasar Denmark ta kudiri aniyya tare da daura damarar hana saye da sayarwar Motoci masu amfani da man fetur da makamashin Gas a shekarar 2030 domin bayar da kofa bude ga Motoci masu amfani da wutar lantarki kadai.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, gwamnatin kasar ta yi wannan yunkuri ne domin rage illolin gurbata iska dake haddasa sauyin yanayi a sanadiyar fitar hayaki daga motoci masu amfani da man fetur da makamashin gas.

Rahotanni sun bayyana cewa, tuni kasar Birtaniya da Faransa sun daura damarar kawo karshen amfani da motoci masu amfani da man fetur da makamashin Gas zuwa shekarar 2040.

Kasar Denmark za ta hana amfani da Motoci masu amfani da Man fetur da makamashin gas

Kasar Denmark za ta hana amfani da Motoci masu amfani da Man fetur da makamashin gas
Source: UGC

Kasashen na ci gaba da jajircewa wajen kawo sauyi da yanayi na juyin juya halin da Motoci masu amfani da wutar lantarki za su mamaye masu amfani da man fetur.

KARANTA KUMA: Babu Tasirin da ficewar Ambode daga APC za ta haifar ga Buhari a jihar Legas - Tinubu

Kazalika Birnin Farisa, Madrid na kasar Andalus da kuma Mexico sun shimfida tsari na hana amfani da motoci masu amfani da man fetur zuwa shekarar 2025 yayin da kasar Faransa ta kudiri makamanciyar wannan aniyya zuwa shekarar 2040.

Legit.ng ta fahimci cewa, tuni dai an fara saye da sayarwar Motoci masu amfani da wutar lantarki a irin kasashen Sweden da Norway da haka ya zamto wani kasafi dak habaka tattalin arzikin kasashen.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel