Babu Tasirin da ficewar Ambode daga APC za ta haifar ga Buhari a jihar Legas - Tinubu

Babu Tasirin da ficewar Ambode daga APC za ta haifar ga Buhari a jihar Legas - Tinubu

A yayin da ake ci gaba da tafka bakin gumurzu sakamakon dambarwar siyasa tsakanin gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode da kuma ubangidansa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, mun samu cewa lamarin ya tumfaya zuwa wani munzali mai tsananin gaske.

Majiyar rahoton a yayin jaddada tsananin rikicin dake tsakanin 'yan siyasar biyu ta bayyana cewa, lamarin ya sanya Tinubu cikin nisa da ya yi maras jin kira ya shaidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ficewar Ambode daga jam'iyyar su ta APC ba za ta haifar da wani tasiri ba a jihar Legas.

Kanwa Uwar gamin matsalolin jam'iyyar ta APC, ya bayar da wannan tabbaci ne yayin ganawarsa da shugaba Buhari a ranar Litinin din da ta gabata. Tinubu ya bayyana cewa ba bu wata illa da rikicin dake tsakanin sa da Ambode zai haifar ga shugaban kasar a jihar Legas yayin zaben 2019.

Babu Tasirin da ficewar Ambode daga APC za ta haifar ga Buhari a jihar Legas - Tinubu

Babu Tasirin da ficewar Ambode daga APC za ta haifar ga Buhari a jihar Legas - Tinubu
Source: Depositphotos

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Tinubu ya bayyana cewa yunkurinsa na hana Ambode samun zarcewa kan kujerar gwamnatin jihar Legas ba zai haifar da wata tangarda ba ga nasarar shugaba Buhari a jihar Legas yayin babban zabe na 2019.

KARANTA KUMA: Gwamna Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Bauchi

Yayin da a ranar da ta gabata shugabancin jam'iyyar APC ya dage zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnan jihar ta Legas zuwa ranar yau ta Talata, mun samu cewa bayan gudanar da zaben shugabancin jam'iyyar ya kuma yi watsi da sakamakon sa.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar, ya lashe zaben fidda gwanin takarar gwamnan jiharsa da aka gudanar a ranar Litinin din da ta gabata.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel