Jam’iyyar APC ta dage zaben tsaida ‘Dan takarar Gwamnan Imo

Jam’iyyar APC ta dage zaben tsaida ‘Dan takarar Gwamnan Imo

Majalisar NWC ta Jamiyyar APC mai mulki ta daga zaben fitar da gwani na Gwamnan Jihar Imo kamar yadda mu ka samu labari dazu ba da dadewa ba. Haka kuma an dage wasu zabukan Jam’iyyar.

Jam’iyyar APC ta dage zaben tsaida ‘Dan takarar Gwamnan Imo

APC ta dage ranar da za ayi zaben Imo da na Sanatoci a Najeriya
Source: Depositphotos

Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC na rikon kwarya Yekini Nabena ya fitar da jawabi inda ya tabbatar da cewa Jam’iyyar ta dakatar da zaben tsaida ‘Dan takarar Gwamna na zabe mai zuwa a Jihar Imo sai nan gaba.

Jam’iyyar ba ta bada wani dalili na dage zaben ba kamar yadda mu ka samu labari. Kafin war haka dai ana rade-radin cewa Sanata Hope Uzodinma yayi nasara a zaben fitar da gwanin inda ya samu kuri’a sama da 420, 000.

Sanatan ya tika Surukin Gwamna mai barin-gado watau Rochas Okorocha wanda ya rantse sai ya kakaba Mijin ‘Diyar sa a matsayin Gwamnan Jihar Imo a 2019. Da alamu dai Surukin Gwamnan watau Uche Nwosu ya sha kasa.

KU KARANTA: Zaben fitar da gwani ya gagari APC a wasu manyan Jihohi 4

Yanzu dai Jam’iyyar tayi watsi da zaben inda ta dakatar da shirin fitar da ‘Dan takarar a APC a Jihar zuwa wani lokaci. Sakataren yada labaran na APC ya kuma bayyana cewa an dage zabukan Sanatoci da aka shirya a fadin kasar.

Kafin zuwan wannan labari dai mun ji cewa Uche Nwosu ya zo na 7 ne a zaben tsaida ‘Dan takarar Gwamna da aka yi a Jihar Imo a karkashin APC. Surukin na Gwamna Okorocha ya tashi da kuri’u 10, 329 ne kacal inji Ahmad Gulak.

Dazu kun ji cewa an dage zaben Gwamna a Jihar Zamfara. Daga cikin masu neman Gwamnan Jihar a APC akwai Ibrahim Wakala, Kabir Marafa, Mansur Dan-Ali, Aminu Sani Jaji, Abu Magaji, Dauda Lawal da Mohammed Sagir Hamidu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel