An matsawa yan takara lamba don su janyewa surikin Buhari

An matsawa yan takara lamba don su janyewa surikin Buhari

Daga cikin kokari da ake yi a ganin an gyarota da kyau don Dr. Mahmod Halilu Ahmed, kanin uwargian shugaban kasa Buhari, Aisha, an matsawa yan takara biyar lamba kan su janye masa takarar sanata na yankin Adamawa ta tsakiya.

Tuni da dama Ahmed ke tseren samun tikitin takarar gwamna da Gwamna Jibrilla Bindow.

Amma bayan alamu sun fara nuna cewa da wuya a kayar da gwamnan, sai ake neman mafita a zai dace da lamarin.

An matsawa yan takara lamba don su janyewa surikin Buhari

An matsawa yan takara lamba don su janyewa surikin Buhari
Source: Depositphotos

An tattaro cewa an tura wakilai hedkwatar jam’iyyar All Progressives Congress(APC) kan cewa kada su tozarta uwargidan shugabankasar da danúwanta.

Daya daga cikin wadanda ke marawa kanin war gidan shugaban kasar ya asance tsohon shugaban kasa wanda ba’a bayyana sunansa ba.

KU KARANTA KUMA: Babban taron PDP: Wike ya gana da Atiku a Port Harcourt

Ya takarar da abun ya shafa sn hada da tsohon manajan darakta na tashar jiragn ruwa, Alhaji Umr Suleiman, tsohon shugaban karamarhukumar Fufre, Barista Aliyu Wakil Boya; tsohon sakataren kungiyar bayar da agaji na Najeriya, Barista Bello Haman Diram; wata tsohuwar mamba a majalisar wakilai, Hon. Aisha Dahiru Ahmed (Binani) da kuma Alhaji Ibrahim Waziri (appa Wazir) wanda ya kasance dan ganin kashenin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zamanin ANPP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel