Yanzu-yanzu: Kwamitin zantarwan jam'iyyar APC ta yi watsi da zaben fidda gwanin jihar Legas

Yanzu-yanzu: Kwamitin zantarwan jam'iyyar APC ta yi watsi da zaben fidda gwanin jihar Legas

Kwamitin gudanarwan jam’iyyar All Progressives Congress APC ta yi watsi da zaben fitar da gwanin gwamnan jihar Legas dake gudana yanzu.

An fara zaben tun da safiyar yau Talata, 2 ga watan Oktoba 2018 a kowani lungu da tsakon jihar Legas.

Legit.ng ta samu rahoton cewa kwamitin gudunarwan ta nisanta kanta da wannan zabe da ke gudana a jihar Legas saboda babu wani wakilin jam’iyyar daga Abuja dake lura da zaben.

Tun da safe, sakamakon zabe ya fara fitowa daga kananan hukumomi amma shugabancin jam’iyyar karkashin Adams Oshiomole tace aikin banza ne.

Zamu kawo muku cikakken rahoton...

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel