Sama da daliban firamari dubu dari uku sun samu tagomashin Buhari a sakkwato

Sama da daliban firamari dubu dari uku sun samu tagomashin Buhari a sakkwato

Jimillan dalibai dubu dari uku da dari da hamsin da daya (300, 151) ne da suka fito daga makarantu firamari daban daban na jahar Sakkwato ne zasu amfana da tsarin ciyarwa kyauta na gwamnatin tarayya a karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ciyar da daliban firamari kyauta na daga cikin kudurorin gwamnatin shugaba Buhari tun kafin ya dare kujerar shugabancin kasar nan, inda yake ganin hakan zai kara ma daliban kwarin gwiwar zuwa makaranta.

KU KARANTA: Duniya ta yi ma wani matashi daurin goro, ya hau saman gada ya tunjuma cikin tafki

Sama da daliban firamari dubu dari uku sun samu tagomashin Buhari a sakkwato

Ciyarwa
Source: Facebook

Majiyarmu ta kara da cewa zuwa yanzu an dauki mata masu girki su dubu biyu da dari tara da talatin da biyu (2, 932) da zasu dafa abincin da gwamnati zata ciyar da daliban, haka zalika makarantu dubu daya da dari takwas da tamanin da daya (1, 881) ne zasu amfana da tsarin.

“Gwamnatin tarayya za ta kula da ciyarwar dalibai yan aji daya zuwa uku, yayin da gwamnatin jaha za ta kula da ciyarwar daliban aji hudu zuwa shida” Inji Alhaji Abdullahi Bala, babban sakatare a ma’aikatar ilimin firamari da na sakandari na jahar.

Sai dai Balan ya samu wakilcin wani darakta a ma’aikatar, Abdullahi Durbawa wanda yace za’a dinga ciyar da daliban abincin naira saba’in a kowanne rana, kuma makarantu 1, 881 ne zasu amfana daga cikin makarantun firamari 2, 015 dake fadin jahar.

Sakataren ma’aikatar ya yaba da wannan tsarin da gwamnatin tarayya ta kirkiro don inganta harkar ilimi, sa’nnan ya bayyana burinsu na ganin ciyarwar ta daure, haka zalika su ma wasu iyayen yara sun bayyana farin cikinsu da wannan cigaba, sa’annan sun yi kira ga ma’aikata da su rike aman.

A wani labarin kuma, shugaba Buhari ya bayyana wannan aikin ciyarwar a matsayin wata hanyar taimaka ma yan kasuwa masu karamin karfi da mata masu rauni, musamman masu girke girke da kuma masu sayar da kayan abinci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel