Da dumi dumi: babban dalilin da yasa shugaba Buhari ya dage zaman majalisar zartarwa

Da dumi dumi: babban dalilin da yasa shugaba Buhari ya dage zaman majalisar zartarwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin dage zaman majalisar zartarwa da ta kunshi kafatanin ministocin gwamnatinsa da wasu zababbun manyan mukarrabansa saboda dalili na siyasa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito fadar gwamnatin tarayya dake Abuja ce ta sanar da haka ta bakin kaakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina wanda yace zaman da aka saba yi a duk ranar Laraba ta kowace sati ba zai yiwu ba a wannan sati.

KU KARANTA: Duniya ta yi ma wani matashi daurin goro, ya hau saman gada ya tunjuma cikin tafki

Da dumi dumi: babban dalilin da yasa shugaba Buhari ya dage zaman majalisar zartarwa

Taron
Source: Facebook

Adesina yace shugaban kasa ya dauki wannan mataki ne sakamakon ana damawa da dama daga cikin ministocinsa a zabukan cikin gida na fitar da yan takarkarun jam’iyyar APC daban daban a jihohinsu, hakan tasa aka dage zaman don basu damar fafatawa a wadannan zabuka.

“Wannan mataki ya tabbata ne sakamakon hidindimun siyasa dake gudana a duk fadin kasarnan, musamman zabukan fitar da yan takarkaru wanda ya hada da dama daga cikin ministocin gwamnatin tarayya.” Inji shi.

Idan za’a tuna, Legit.ng ta ruwaito wasu ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari sun tunkuyi kasa a wajen tantance yan siyasa dake sha’awar shiga takarar mukamai daban daban a jihohi daban daban.

Wadannan ministocin Buharin sun hada da ministan sadarwa, Adebayo Shittu wanda kwamitin tantancewar ta haramta masa takara saboda rashin yin hidimar kasa bayan ya kammala karatun digiri, da kuma ministar al’amuran mata, Aisha Alhassan wanda tuni ta yi murabus daga gwamnatin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel