Tsokacin Amurka kan zabukan Najeriya da ke tafe gadan-gadan

Tsokacin Amurka kan zabukan Najeriya da ke tafe gadan-gadan

- Zabukan Najeriya saura wata hudu da rabi a yi su kaf!

- A zabukan kasashen Afirka, ana yawan samun matsalolin tsaro

- Anyi kira ga duniya ta sa ido sosai kan zabukan Najeriya don gudun me kaa-je-yazo

Tsokacin Amurka kan zabukan Najeriya da ke tafe gadan-gadan

Tsokacin Amurka kan zabukan Najeriya da ke tafe gadan-gadan
Source: Depositphotos

A sakon taya murna da Mista M. Pompeo ya rattaba wa Najeriya, Ministan harkokin wajen Amurka, a yayin da yake taya kasar nan murnan cika shekaru 58 da haifuwa, bayan mulkin mallakar turawan Ingila, ya ce kasar Najeriya abokiyar qut-da-qut ce ta fannoni da dama.

Ya yaba da kuma yadda kasar ta dore bisa siratsin dimokuradiyya mai dorewa, inda ya sha alwashin agazawa kasar nan kan samar da zabuka na gari a badi mai kamawa.

DUBA WANNAN: Lakcara ya bingire ya adi saboda rashin albashi, ya mutu

A sakon nasa, yayi kira ga 'yan Najeriya da 'yan siyasa, da su dinga cizawa suna hurawa, domin kujewa rikici yayin zabe.

A 2015 ma dai, sai da AMurkar tayi irin wannan kashedin don kar a tada kayar baya ko a tada rikici, ga wadanda suka fadi zabe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel