Kimiyya: Anyi nasarar raba lange-lange da iya raba cutar maleriya a dakin kimiyya

Kimiyya: Anyi nasarar raba lange-lange da iya raba cutar maleriya a dakin kimiyya

- Lange-Lange mai ramar qeta, kowa ya kai mari duhu kai ya jiwo

- An gano Sauro ke kawo zazzabin Malariya ne a shekaru 200 da suka wuce

- A zamanin da an dauka zazzabi zunubi ke kawo shi

Kimiyya: Anyi nasarar raba lange-lange da iya raba cutar maleriya a dakin kimiyya

Kimiyya: Anyi nasarar raba lange-lange da iya raba cutar maleriya a dakin kimiyya
Source: UGC

Sauro dai, an gano ashe shi yake kawo cutar zazzabin bayan an shafe dubban shekaru ana yanka ko addu'a kan neman waraka daga cutar da ba'a fahimceta ba a baya.

Babu halittar da ta yiwa dan'adam barna a tarihinsa na shekaru 200,000 a duniya irin sauro, dan mitsili sai dabara.

Macen sauro ce dai kadai take shan jini, namijin fulawa da tsirrai yake tsotsa, tana bukatar jinin ne don itama ta sami damar hada kwayayenta don yaada iyali.

Barbara daya tal macen kanyi da namiji, inda takan adana maniyyinsa har tsawon rayuwarta, sai dai tayi amfano da shi lokacin saka kwai, bayan ta cika cikinta da jini.

DUBA WANNAN: Lakcara ya bingire ya adi saboda rashin albashi, ya mutu

Garin shan jini ne sukan saki kwayoyin cutar Protozoa, wadda kan bi jini taje hanta ta haifu, har a sami cutar maleriya bayan makonni.

Cikin nau'o'in sauro da ake dasu a duniya 3500, 40 ne kacal ke iya yada cutar maleriya, wasunsu kuma, zika virus mai baiwa yara mitsilin kai.

An sami sa'ar raba macen Anopheles Gambiae ta nau'in sauro mai janyo maleriya a kimiyyance, bayan da aka sauya kwayoyin halittarsu na tsawon hayayyafa har 11.

Masanan da suka yi aikin, sunce yanzu kam, anyi nasarar hana ta bukatar haihuwa ne kacokan, wadda dama sai tana da kwai ne zata nemi jini.

In anci nasara dai an fadada shirin, inda za'adinga yin hakan ana sakin sauron cikin al'ummar suro, don su yadu cikinsu da wannan naqasu, wadda zata kai ga kade cutar zazzabin maleriyas gaba daya daga doron kasa, da ya addabi jama'a musamman a Afirka.

Ana can yanzu haka a Ingilla a jami'ar Imperial College, a inda aka yi binciken ana sowa, ganin an fara amfani da wannan kimiyya don sauya wa 'yan Afirka rayuwa, zuwa mai dorewa, maimakon ta rufa-ido da camfe-camfe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel