Lakcara ya fadi ya mutu bayan an kasa biyansa albashi a jihar Kogi

Lakcara ya fadi ya mutu bayan an kasa biyansa albashi a jihar Kogi

- Tun bara ba'a biya shi salare ba

- Ya yanke jiki ya fadi ya mutu

- Gwamnatin Kogi ta dade bata iya biyan bashi a jihar

Lakcara ya fadi ya mutu bayan an kasa biyansa albashi a jihar Kogi

Lakcara ya fadi ya mutu bayan an kasa biyansa albashi a jihar Kogi
Source: UGC

Duk da bikin bude sabuwar fada da gwamnan jihar Kogi yayi a kayuensu, jim kadan bayan da ya dare gwamnan jihar Kogin a kyauta, gwamnan, ya kasa biyan albashin ma'aikata inda ya dauki tsawon lokaci yana aikin tantance su.

A irin haka ne, wasu da yawa suka ma mutu suka huta da wannan wahala ta albashin jihar Kogi da ma wasu jihohin.

Malam Yakubu na-ta'ala dai, lakcara ne a Poly ta jihar Kogi, wanda tun watan Yuli bai qara jin alert na albashi a wayar sa ba.

Kwatsam, jiya ana zaune kawai sai ya bingire ya fadi, nan take kuwa yace ga garinku nan, lamari da aka danganta da irin bakar wahala da fatara da ya fada saboda rashin kudi da biyansa hakkokinsa.

DUBA WANNAN: NNPC ya dan farado da riba

Sai dai mai magana da yawun makarantar, Luka Tijjani, yace Malamin, ya rasu ne saboda bayan an masa tiyata don cire matsarmamar afendis daga jikinsa, ya sami 'yar mishkila, wadda aka kasa magance ta.

Ya ma tabbatar da cewa, lallai malamin na daga cikin wadanda basu sami gwamnati ta biya su kudinsu ba tun bara.

Rashin kudi a aljihu dai, yana iya cefa mutum cikin zullumi, ko fatara, har ma da gaza samun abinci mai gina jiki, wanda ka iya jawo cuta ko ajali.

Allah-kyauta!

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel