2019: Buhari zai sha mamaki daga 'yan Najeriya a zaben badi - Fayose

2019: Buhari zai sha mamaki daga 'yan Najeriya a zaben badi - Fayose

- Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose, yace yan Najeriya zasu ba ma shugaban kasa Muhammadu Buhari mamaki a zaben 2019

- Ba jam'iyyun adawa kadai zasu kada Buhari ba

- Ginshikan Gwamnatin Buhari sun dadewa da faduwa

2019: Buhari zai sha mamaki daga 'yan Najeriya a zaben badi - Fayose

2019: Buhari zai sha mamaki daga 'yan Najeriya a zaben badi - Fayose
Source: UGC

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yace zaben 2019 zai kasance fada ne tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da yan Najeriya da suka gaji da mulkin shi.

A jiya ne mai taimakon na musamman ga gwamnan na kafafen sadarwa, Lere Olayinka, ya bayyana hakan. Gwamnan yace ba jam'iyyar PDP ce zata ba Shugaban kasar mamaki ba, ko sauran jam'iyyun adawa kadai ba, har da yan kasar Najeriya.

Fayose yace ginshikan da mulkin shugaban suke tsare a kai, su dade da rushewa. Kasashen ketare ma sun tabbatar da cewa rashawa dake a cikin mulkin shugaban, ta wuce wacce akwai a da.

Yan Najeriya kansu sun San an samu karin ta'addancin fulani makiyaya, bayan Boko Haram. Tattalin arziki kuma da yake bunkasa a lokacin Goodluck Jonathan, ya samu tabarbarewa tare da lalacewa a karkashin shugabancin Buhari.

DUBA WANNAN: Nuhu Ribadu ya dawo takarar gwamna

"Ga yan Najeriya, zaben 2019 ba na jam'iyya bane kadai, na kawo karshen mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne," inji Fayose.

Kamar yadda gwamnan yace, miliyoyin yan Najeriya sun rasa aiyukan su, kamfanoni marasa adadi ake rufewa a kullum don haka yan Najeriya suke shirye suna jiran zaben 2019 domin huce fushi tare da takaicin da shugaban kasar ya sa su ciki.

"Buhari ya tsawwala wa rayukan yan Najeriya, sun dena yarda da shi ta fannin zabe ma, don haka dole ne su kayar dashi a zabe mai zuwa don samo kan kasar, " inji Fayose.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel