Fasinjoji 15 sun gamu da ajalinsu bayan da motarsu ta kama da wuta a kusa da Abaji

Fasinjoji 15 sun gamu da ajalinsu bayan da motarsu ta kama da wuta a kusa da Abaji

- Fasinjoji 15 sun gamu da ajalinsu bayan da motar da suke ciki kirar Bas ta kone kurmus a safiyar ranar Litinin a kauyen Manderegi

- Rahotanni sun bayyana cewa sitiyarin motar ya kwace a hannun direban, wanda hakan ya sa motar ta afkawa tirelar da ke a bakin titin

- Sai dai jama'ar garin Manderegi sun samu nasarar ceto fasinja daya 'tilo' wanda ya samu raunuka

Fasinjoji 15 sun gamu da ajalinsu bayan da motar da suke ciki kirar Bas ta kone kurmus a safiyar ranar Litinin a kauyen Manderegi, kusa da garin Abaji da kan hanyar Abuja zuwa Lokoja. Wani da lamarin ya afku a gabansa, Saidu, ya shaida cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2 na dare.

Saidu ya ce motar mai cin mutane 18 na dauke da lambar mota: RNG 818 XA, ta kwacewa direban inda ta afka wa wata tirela da ke ajiye a bakin titin mai lambar mota: DKA 871 ZU.

Ya ce bas din ta fito ne daga hanyar Lokoja a lokacin da sitiyarin motar ya kwace a hannun direban, wanda hakan ya sa motar ta afkawa tirelar.

"Nan take bas din ta kama da wuta. Mutanen kauyen sun fito don ceto rayukan mutanen ciki amma hakan ya faskara. Sai dai, mun samu nasarar ceto mutum daya daga cikinsu," a cewar sa.

Fasinjoji 15 sun gamu da ajalinsu bayan da motarsu ta kama da wuta a kusa da Abaji

Fasinjoji 15 sun gamu da ajalinsu bayan da motarsu ta kama da wuta a kusa da Abaji

Ya kara da cewa a lokacin da direban tirelar da yaransa biyu suka ga motar ta kama da wuta, sai suka raba kan tirelar da bodinta, suka gudu ba tare da sun tsaya ganin yadda lamarin zai kasance ba.

Wakilin Dailytrust da ya isa wajen da lamarin ya faru, da misalin karfe 8 na safiya, ya kirga gawarwakin mutane 18, a lokacin da jami'an hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ke sauyawa masu ababen hawa hanyar da za su bi.

Ko da aka tuntubi kwamandan rundunar FRSC na garin Abaji, Olasupo Esuruoso, ya tabbatar da faruwar hatsarin, ya kuma ce tuni aka mika gawar mutanen ga iyalansu don yi masu sutura, haka zalika fasinja daya 'tilo' da ya tsira an garzaya da shi asibitin koyarwa na jami'ar Abuja da ke Gwagwalada.

Babbar Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel