Yanzu Yanzu: Masu zanga-zanga sun mamaye sakatariyar APC a Ekiti

Yanzu Yanzu: Masu zanga-zanga sun mamaye sakatariyar APC a Ekiti

A ranar Talata, 2 ga watan Oktoba, masu zanga zanga sun mamaye satariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dake Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

Channels TV sun ruwaito cewa masu zanga-zangar na Allah wadai ne da gudanar da zaben fidda wakilai a matakin karshe na fitar da yan takarar majalisun dokokin kasa.

Yanzu Yanzu: Masu zanga-zanga sun mamaye sakatariyar APC a Ekiti

Yanzu Yanzu: Masu zanga-zanga sun mamaye sakatariyar APC a Ekiti
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa da farko kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun amince da amfani ne da zaben fidda gwani na kato-bayan-kato a majalisun dokokin kasar a jihar.

A wani lamari makamancin haka mun ji cewa, wasu fusatattun mutane a ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba sun hana Gwamna Muhammed Abubakar jefa kuri’a a mazabarsa lokacin zaben fidda gwani na gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Tambuwal na zawarcin wakilan jihar Buhari

An hargitsa zaben wanda ya gudana a kananan hukumomi daban-daban na jihar sannan an kasa gudanar da zaben.

Sakamakon haka, wasu yan takara suka janye daga tseren sannan suka bukaci a soke zaben cewa basu aminta da tsarin ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel