Zaben 2019: Tambuwal na zawarcin wakilan jihar Buhari

Zaben 2019: Tambuwal na zawarcin wakilan jihar Buhari

Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya mika kokon bararsa ga tawagar jam’iyyar daga jihar Katsina don su zabe shi a babban taron jam’iyyar da za’a gudanar.

Tambuwal dai na adawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya kasance dan asalin jihar Katsina kuma yake neman takarar kejarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Tambuwal wanda ya gana da wakilai jam’iyyar PDP a jihar, yace jihar Katsina wacca ta samar da wasu shugabanni da ake ganin girmansu sosai bata chanchanci abunda ke gudana a yanzu ba.

Zaben 2019: Tambuwal na zawarcin wakilan jihar Buhari

Zaben 2019: Tambuwal na zawarcin wakilan jihar Buhari
Source: Facebook

Tambuwal a wata sanarwa dauke das a hannun kakakin kungiyar kamfen din shi, Dr. Okey Ikechukwu ya bukaci tawagar da su taya shi fafutukar wannan kujera.

KU KARANTA KUMA: KAI TSAYE: Zaben fidda gwanin jihar Legas, sakamako sun fara shigowa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Talata, 2 ga watan Oktoba wasu masu zanga—zanga sun karade unguwannin jihar Kogi yayinda Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya kai ziyara jihar. Masu zanga-zangar da yawa sun mamaye sakatariyar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) jihar Kogi dake Lokoja, inda suka hargitsa ziyarar kamfen din da Saraki ya kai.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Saraki ya je Kogi domin zawargin wakilan jamiyyar gabannin zaben fidda gwanin jam’iyyar inda yake muradin mallakar tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel