Zanga-zanga ya bata ziyarar da Saraki ya kai Kogi

Zanga-zanga ya bata ziyarar da Saraki ya kai Kogi

A ranar Talata, 2 ga watan Oktoba wasu masu zanga—zanga sun karade unguwannin jihar Kogi yayinda Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya kai ziyara jihar.

Masu zanga-zangar da yawa sun mamaye sakatariyar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) jihar Kogi dake Lokoja, inda suka hargitsa ziyarar kamfen din da Saraki ya kai.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Saraki ya je Kogi domin zawargin wakilan jamiyyar gabannin zaben fidda gwanin jam’iyyar inda yake muradin mallakar tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Zanga-zanga ya bata ziyarar da Saraki ya kai Kogi

Zanga-zanga ya bata ziyarar da Saraki ya kai Kogi
Source: UGC

Masu zanga zangar na dake dauke a kwalayen sanarwa kamar “Bamu yadda da tursasawa ba”, “Kada ku kakaba mana Dino”, “Ku bari ayi zaben fidda gwani na gaskiya”, “Kogi ba Kwara bane”.

Sun bukaci Sgaban majalisar dattawa da kada ya kakaba masu Sanata Dinbo Melaye a Kogi na yamma, abunda suke ganin kamar Saraki ne ya shirya shi.

KU KARANTA KUMA: Zaben fidda gwani na APC: Fusatattun mutane sun hana Gwamnan Bauchi kada kuri’a

Suna zanga-zanga ne kan zargin cewa ana kokarin ba Dino Melaye tikitin takara kai tsaye.

A nashi martanin, Saraki yayi alkawarin cewa idan yayi nasarar zama shugaban kasar Najeriya zai daidaita lamura.

Yayi alkawarin inganta rayuwar yan Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel