Ezekwesili: An mayar da rayukan 'yan Nigeria kamar na kiyashi a yau

Ezekwesili: An mayar da rayukan 'yan Nigeria kamar na kiyashi a yau

- Shugabar kungiyar BBGC, Mrs Oby Ezekwesili, ta ce an mayar da rayukan 'yan Nigeria kamar kiyashi a kasar nan

- Ta kalubalanci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na gaza kare rayukan 'yan Nigeria da dukiyoyinsu

- Ezekwesili ta yi kira da a samar da wani taron gaggawa na kwararru da zasu shawo kan wannan matsalolin tsaro a kasar

Shugabar kungiyar shirin fafutukar dawo da 'yan matan da 'yan tada kayar baya na Boko Haram suka yi garkuwa da su, "Bring Back our Girls Campaign", Mrs Oby Ezekwesili, ta ce an mayar da rayukan 'yan Nigeria kamar kiyashi a kasar nan a yau.

Ezekwesili ta bayyana hakan a daren ranar litinin, a wata hira da tayi da gidan talabijin na Channel News, a cikin wani shiri na musamman kan bukin murnar cikar Nigeria shekaru 58 da samun 'yanci daga mulkin turawan mallaka.

Ta ce abun takaici ne da tayar da hankali yadda aka mayar da rayukan 'yan Nigeria kamar kiyashi, musamman ma marasa galihu, inda har akan bijiro da tambayar, "Nawa ne darajar rayukan 'yan Nigeria a yau?"

KARANTA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta yi Allah-wadai da sabon rikicin Jos

Ezekwesili: An mayar da rayukan 'yan Nigeria kamar kiyashi a yau

Ezekwesili: An mayar da rayukan 'yan Nigeria kamar kiyashi a yau
Source: Depositphotos

Ezekwesili, wacce ta taba rike mukamin ministar ilimi a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ta kalubalanci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na gaza kare rayukan 'yan Nigeria da dukiyoyinsu.

Haka zalika ta kuma koka dangane da yadda mutane suke mayar da rasa rayukan mutane kamar ba a bakin komai ba a lokacin da suke rubuta rahoto akan hakan, musamman ta yadda suke cewa "an rasa rayukan mutane 14 kawai", tana mai cewa "Ta ya zamu gina al'umma da ba su ganin darajar rayukan 'yan uwansu?"

A ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a kasar, Ezekwesili ta yi kira da a samar da wani zaman gaggawa na kwararru da zasu shawo kan wannan matsalar.

Babbar Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel