Zaben fidda gwani na APC: Fusatattun mutane sun hana Gwamnan Bauchi kada kuri’a

Zaben fidda gwani na APC: Fusatattun mutane sun hana Gwamnan Bauchi kada kuri’a

Wasu fusatattun mutane a ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba sun hana Gwamna Muhammed Abubakar jefa kuri’a a mazabarsa lokacin zaben fidda gwani na gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

An hargitsa zaben wanda ya gudana a kananan hukumomi daban-daban na jihar sannan an kasa gudanar da zaben.

Sakamakon haka, wasu yan takara suka janye daga tseren sannan suka bukaci a soke zaben cewa basu aminta da tsarin ba.

Zaben fidda gwani na APC: Fusatattun mutane sun hana Gwamnan Bauchi kada kuri’a

Zaben fidda gwani na APC: Fusatattun mutane sun hana Gwamnan Bauchi kada kuri’a
Source: Depositphotos

A halin da ake ciki, mun ji cewa an kashe mutun daya a Boi, karamar hukumar Bogoro dake jihar Bauchi a ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba yayinda yake kokarin jefa kuri’a a zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) yayinda biyu ke asibiti bayan wasu mutane da ba’a sani ba sun yi harbi.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya bayyana dalilin da ya sanya masu madafan iko ke masa adawa

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa yan takarar gwamna a APC dake takara a zaben fidda gwani, Yakubu Ibrahim Lame, da Mohammed Ali Pate sunyi zarge-zarge yayinda suke jawabi ga manema labarai a taron NUJ a yammacin ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba, kan yadda aka gudanar da shirin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel