Bayan janyewarsa, yanzu dai Nuhu Ribadu ya dawo takarar gwamna gadan-gadan a APC

Bayan janyewarsa, yanzu dai Nuhu Ribadu ya dawo takarar gwamna gadan-gadan a APC

- Tsohon shugaban EFCC ya bayyana son shiga zaben fidda gwani bayan ya fita a ranar lahadi

- A ranar lahadi ne yakamata ayi zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Adamawa

- A yanzu shirye yake da ya shiga cikin jerin yan takarar

Bayan janyewarsa, yanzu dai Nuhu Ribadu ya dawo takarar gwamna gadan-gadan a APC

Bayan janyewarsa, yanzu dai Nuhu Ribadu ya dawo takarar gwamna gadan-gadan a APC
Source: Twitter

Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa EFCC, Malam Nuhu Ribadu, ya nuna son komawa cikin jerin manema kujerar shugabancin jihar Adamawa karkashin jam'iyyar APC.

Da farko ya janye ne a ranar lahadin da ta gabata, inda daga baya kuma ya bayyana bukatar shi ta komawa cikin maneman bayan da aka maida zaben ranar Alhamis mai zuwa.

Alhaji Salihu Bawuro, darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a taron manema labarai d akayi a Yola, a ranar litinin.

Bawuro yace kungiyar yakin neman zaben ta gamsu da hukuncin da shugabannin jam'iyyar suka yanke na maida zaben zuwa ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: Gingimari ta fashe da mai a tanki a Legas, ta kashe mutane

"Yanzu shugabannin jam'iyyar na kasa sun shigo lamarin domin gyara, Malam Nuhu Ribadu kuma zai fito domin zaben fidda gwanin tunda an maida shi Kato bayan Kato " inji Bawuro.

Yace kungiyar ta shirya domin zaben dake gabatowa, kuma zatayi duk kokarin da yakamata don ganin komai ya tafi lafiya lau.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel