NNPC taci ribar N18.12b a wata daya kacal, fiye da dukkan na baya

NNPC taci ribar N18.12b a wata daya kacal, fiye da dukkan na baya

- An sami uwar riba a NNPC a wannan karo

- Ribar ta samu ne don an sami karin yawan mai kusan ganga 2m

- An maida NNPC saniyar tatsa a gwamnati

NNPC taci ribar N18.12b a wata daya kacal, fiye da dukkan na baya

NNPC taci ribar N18.12b a wata daya kacal, fiye da dukkan na baya
Source: UGC

Kamfanin hada-hadar mai na kasa, watau NNPC ya saki rahotonsa na wata-wata, inda ya nuna a watan, ya sami ribar N18, qarin biliyan daya a watan Mayu fiye da watan Afrilu a bana.

A cewar kamfanin, kudaden sun sami karuwa ne bayan da aka sami habakar farashin mai a duniya, dama kuma yadda aka sami zaman lafiya a yankin Neja Delta.

DUBA WANNAN: Gingimari ta fashe da mai a tanki a Legas, ta kashe mutane

Kamfanin, yace ribar ta hada da kudaden da ake samowa daga sauran kamfunna dake karkashin kamfanin, kamar dai su PPMC, DPR da PPPRA.

Najeriya dai ta dogara da man etur ne kacokan, wajen samun kudaden da ake rabawa jihohi, wanda suma dashi suke dogara kafin su tsaya da kafafunsu, shekaru kusan 60 da kafa kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel