Bidiyo: Ta faru ta kare, mutan jihar Legas sun juyawa gwamna Ambode baya, sunyi biyayya ga Tinubu (Bidiyo)

Bidiyo: Ta faru ta kare, mutan jihar Legas sun juyawa gwamna Ambode baya, sunyi biyayya ga Tinubu (Bidiyo)

Faifan bidiyo ya nuna babu wanda ke shirin zaben gwamnan jihar Legas na yanzu, Akinwumi Ambode, a zaben fitar da gwanin da ke gudana a yau Talata, 2 ga watan Oktoba 2018 a jihar Legas.

A makonnin da suka gabata, mun kawo muku rahoton cewa babban Jigon Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya ki marawa Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode baya a zabe mai zuwa da za ayi. Majalisar GAC da ke ba Gwamna shawara dai ta ki dafawa Mai Girma Ambode.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Majalisar ta GAC wanda ita ce koli wajen duk wani mataki da za a dauka a siyasar Legas ta tashi zaman ta wannan makon inda ta nuna cewa dole ayi zaben kato-bayan-kato a Jam’iyyar APC a Legas.

'Yan majalisar jihar Legas sun juya wa gwamna Akinwumi Ambode baya yayin da 36 cikin 40 na mambobin suka marawa Babajide Sanwo-Olu baya a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar a zaben 2019.

'Yan majalisan sun bayyana matsayansu ne bayan wata taro da su kayi a yau Asabar karkashin jagorancin Kakakin majalisar jihar, Mudashiru Obasa inda dukkan 'yan majalisar suka sanya hannu a takarda.

Kazalika, daya daga cikin masu neman takarar gwamna jihar Legas karkashin jam'iyyar APC, Obafemi Hamzat shima ya janye takararsa tare da marawa Sanwo-Olu baya.

Kalli bidiyon:

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel