2019:Chris Okotie ya shiga tseren neman takarar shugaban kasa

2019:Chris Okotie ya shiga tseren neman takarar shugaban kasa

- Reverend Chris Okotie ya bayyana kudirinsa na son takarar kujeran shugaban kasa a zabe mai zuwa

- Ya tuntubi sauran jam’iyyun siyasa da su zabe shi a matsayin dan takara na hadin gwiwa

- Okotie yace lokaci yayi da ya kamata a rungumi sabon shugaba da zai ceto kasar

Wani babban fasto kuma shugaban cocin Household of God Church International Ministries, Reverend Chris Okotie, ya shiga tseren kujerar shugabancin kasa na 2019.

Babban malamin addinin ya bayyana kudirinsa na shiga tseren kujerar shugabancin kasar a ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba a lokacin bikin ranar samun yancin kan Najeriya na 58, Channels ta ruwaito.

2019:Chris Okotie ya shiga tseren neman takarar shugaban kasa

2019:Chris Okotie ya shiga tseren neman takarar shugaban kasa
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa Okotie ya bayyana cewa zai yi takara ne a karkashin jam’iyyar Fresh Democratic Party.

Ya kuma yi amfani da damar ya tuntubi sauran jam’iyyun siyasa da su zabe shi a matsayin dan takara na hadin gwiwa.

Idan za ku tuna a baya Legit.ng ta rahoto cewa Reverend Chris Okotie ya yi kira ga manyan jam’iyyun siyasar kasar - All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) – da su dauke shi a matsayin dan takararsu.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun dakarar da zaben fidda gwani na PDP da Kwankwasiyya ke jagoranta a Kano

Okotie da yake Magana a taron manema labarai a cocinsa a ranar Lahadi, 15 ga watan Yuli ya bukaci ýan Najeriya da suyi gaggawar tabbatar da mafarkin Najeriya inda lissafo abubuwan da suka tabarbare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel