Yan sanda sun dakarar da zaben fidda gwani na PDP da Kwankwasiyya ke jagoranta a Kano

Yan sanda sun dakarar da zaben fidda gwani na PDP da Kwankwasiyya ke jagoranta a Kano

Rundunar yan sanda sun tarwatsa zaben fidda gwani na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda bangaren Kwankwasiyya ke gudanarwa a Kano a jiya Litinin, 1 ga watan Oktoba.

Yan sanda sun hana daruruwan magoya bayan kwankwasiyya da suka taru a sakatariyar Lugard House shiga cikin ginin wanda suka yiwa kawanya tun da misalin karfe 06:00 na safe.

Babban sakataren kungiyar Kwankwasiyya na kasa, Kwamrad Auwal Muhammad ya bayyana cewa sun kasance a Lugard House domin a tantance tawagarsu da yan takararsu dake shirin zaben fidda gwani.

Yan sanda sun dakarar da zaben fidda gwani na PDP da Kwankwasiyya ke jagoranta a Kano

Yan sanda sun dakarar da zaben fidda gwani na PDP da Kwankwasiyya ke jagoranta a Kano
Source: Twitter

"An bukaci dukkanin wakilai da yan takarar Kwankwasiyya su tattaru a Lugard House a yau domin tantancewar karshe kafin zaben fidda gwani,” inji shi.

“Wannan ya kasance gida da mukan gudanar da taronmu sannan mu tattauna akan lamuran siyasa. Don haka an gayyaci PDP da sauran gamayyar Kwankwasiya daa kananan hukumomi 44 kawai sai muka zo muka tarar da jami’an yan sanda sunyiwa gidan kawanya,” cewar shi.

Masu kawo mana rahoto sun lura cewa kimanin motocin yan sanda bakwai ne suka taru a yankin Marhaba, wanda zai sada ka dad akin taron, yayinda aka tura biyar zuwa Lugard House, inda suka kewaye duk hanyoyin da zai sada mutun dad akin taron.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai hari garuruwan Jos an kashe mutane 7

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar Kano, SP Magahi Musa Majia, yace yan sanda na bin umurnin kotu ne da ta hana PDP gudanar da zaben fidda gwani ko duk wani harkokin siyasa a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel